Hamshaqin attajirinnan na nahiyar Afrika kuma dan asalin Najeriya ya bayyana cewar a 2021 yana da burin sayen kungiyar kwallon kafa ta Arsenal.
Tun a shekara ta 2018 Dangote yake yunkurin sayen kungiyar kwallon kafan amma hakansa bai cimma ruwa ba.
Dangote dai nadaga cikin magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a duniya kuma kome akayiwa Arsenal shima yana shanyewa.
Ayanzu dai an bayyana Dangote amatsayin attajirin daya mallaki kudi sama da £8.5 billiyan inda yace badan yana kan ganiyar gina kamfanin sa na Lagos ba to da a shekarar nan ma zai tunkari sayen kungiyar.
Dangote ya kara da cewa magoya baya nata korafi akan shugaban kungiyar na yanzu wato Stan Kroenke na rashin sakin kudi yayi abin dayadace amma idan muka saya to za a warwasa wannan sunan da ake gayamana na kofi haram zaizama tarihi.
Daga karshe magoya bayan Arsenal sun bayyana cewar canji biyune zai tabbata a kungiyar wato tunda an canja Unai Emery an kawo Arteta to shima shugaban kungiyar ta Arsenal so suke a canzashi.