Shekaru 55 Bayan Rasuwar Sardauna: Waye Magajinsa?

1766

Wanene Sardaunan Sokoto?

An haifi Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, a ranar 12 ga watan Yuni na 1910 a garin Rabbar na jihar Sokoto.

Kakansa shi ne sarkin Musulmi Bello, wanda na daya daga cikin wadanda suka kafa daular Sokoto, kuma dane ga marigayi Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodiyo.

Ahmadu Bello ya fara makaranta a garin Sokoto, sannan ya wuce zuwa makarantar horas da malamai ta Katsina.

Kafin daga bisani Sultan ya nada shi malami a makarantar Middle School ta Sokoto.

A shekarar 1938 aka nada shi Sardaunan Sokoto bayan da ya gaza a yunkurin da yayi na zamowa Sultan, wato Sarkin Musulmi.

Ya kuma halarci kasar Ingila domin yin karantu kan harkokin mulki a shekarar 1948.

Ya kuma fara shiga harkokin siyasa gadan-gadan bayan dawowarsa daga karatu, inda har aka zabe shi ya zamo mamba a majalisar dokoki ta Arewacin Najeriya. Ya kuma zama ministan ayyuka da raya kasa.

Ya kasance Firimiyan farko na yankin Arewa daga shekarar 1954 zuwa 1966.

Sannan ya jagoranci jam’iyyar NPC ta lashe kujeru da dama a zaben da aka gudanar bayan samun ‘yancin kai.

Bayan kammala zabe, ya zabi ya ci gaba da kasancewa Firimiya, inda ya nada Abubakar Tafawa Balewa ya zamo Fira Minista.

Sardauna Da Kishin Arewa

Ya taka rawa sosai wajen hada kan yankin Arewacin kasar nan wanda ke da ƙabilu mabiya addini daban-daban, da kuma aiwatar da ayyuka na ci gaban kasa.

Irin gudunmuwar da Sardauna ya bayar wajen ci gaban yankin arewacin ƙasar nan ya sa ya zama abin misali da kwaikwayo a sassan yankin.

Tarihi ya nuna cewa Sardauna mutum ne da ba ya nuna wariyar addini ko kabilanci ko kuma ta yanki.

Wata tambaya da ta fi jan hankulan masharhanta ita ce, shin mene ne ya sa har yanzu Sardauna ke ci gaba da zama abin kwatance da zama a zukatan mutane shekaru 54 bayan rasuwarsa?

La’akari da irin yadda ake ta samun ƴan siyasa da masu riƙe da muƙaman da ka iya cewa Sardauna Ahmadu Bello ne silar iliminsu, amma yau sun yi watsi da duk wata koyarwarsa tare da tarbiyyar gina yankin arewacin ƙasar nan.

Babu shakka a bayyane take za ka dinga ana ta naɗa sarautar SARADAUNA amma inda gizo ke saƙar da yawa daga cikin waɗanda ake baiwa wannan Sarauta ta SARADAUNA ba su ko haɗa hanya da kishi da halin ƙwarai irin na asalin ba.

Aiyukan Da Sardauna Ya Yiwa Arewa

Gudummuwarsa kan harkokin ilimi, inda ya ba da umarnin gina makarantun firamare da sakandare har da na gaba da sakandare da jami’a.

Daga cikin makarantun da ya kaddamar da bikin bude su har da Makarantar Horon Malamai ta Wudil a jihar Kano, a ranar 27 Nuwamba 1965.


Ya bude Kwalejin Horon ’Yan sanda ta Kaduna a ranar 30 Nuwamba, 1963. Ya bude Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Kaduna (Polytechnic) da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Samaru Zariya a ranar 11 Oktoba 1962.


A fannin ruwan sha da noma ga jama’a, Firimiyan ya gina madatsun ruwa domin noman rani da kiwo, ma’aikatun ruwa da rijiyoyi a lardunan Arewa.

Ya kaddamar da bude Ma’aikatar Ruwa ta Daura a ranar 23 ga Nuwamba, 1960. Ya bude Ma’aikatar Ruwa ta Mando-Kaduna a ranar 25 ga Maris 1960.


A fannin lafiya, Firimiyan ya gina asibitoci a larduna da asibitin kashi guda daya tilo a Dala da ke birnin Kano a ranar 21 Disamba 1959. Asibitin da ya dauki nauyin kula da majinyata kashi daga jihohin Arewa 19.

A fannin tattalin arzikin kasa, Firimiyan Arewa ya gina bankuna, ya bude Bankin Baclyas da yanzu ake kira Bankin Al’umma (Union Bank) na farko a Arewa a ranar 15 Satumba 1956.

Haka ma shi ne ya bude Bankin Arewa (Bank of the North) da aka mai da shi Unibersal Bank.

Ya bude Hukumar Wutar Lantarki ta Arewa (ECN) a garin Bida a ranar 1 ga Janairu 1961.

Ya kuma bude otel din Hamdala da ke garin Kaduna a ranar 27 ga Fabrairu 1960.


Sauran nasarorin da Firimiyan Arewa ya samu sun hada har da bude kamfanin buga jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo. Da kamfanin simunti na Arewa a Sakkwato da Masakar Arewa a Kaduna da ta Gusau da Gidan Rediyo da Talabijin na Kaduna (Farin Gida) da filin wasa na Kaduna da sauransu.

An kashe Ahmadu Bello a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 1966, bayan wani juyin mulki da wasu sojoji ‘yan kabilar Ibo suka jagoranta.

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan