Tsohon Shugaban Ƙasar Amurka Obama Zai Tsaya Takarar Shugabancin Ƙasar Kenya

1771

Tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama ya shirya kafa babban tarihi a duniya a fannin siyasa.

A safiyar yau ne tsohon shugaban kasar ya bayyana kudurinsa na fitowa takarar shugaban kasar Kenya a shekarar 2021.

Barack Obama wanda yake da ne a wajen wani mai fada aji a kasar Kenya, yayi mulkin kasar Amurka daga shekarar 2009 zuwa 2017, Obama shine shugaban kasa na 44 a tarihin kasar Amurka.

A yayin wata ziyara da ya kai birnin Mombasa dake kasar ta Kenya, Obama ya samu tarba ta mutane masu yawan gaske wadanda suke nuna masa tsantsar soyayya. Tsananin yawan mutane da suka ziyarci wajen tarba tsohon shugaban kasar ya sanya ya bayyana cewa zai dawo siyasa.

“Na gaji da siyasar kasar Amurka, bayan ina ganin yadda kasar Kenya ke faman wahala. Ina ganin ya kamata nayi wani abu da zan taimakawa kasa.”

Tsohon shugaban kasar Amurkan ya bayyana cewa yana da tabbacin cewa zai iya taimakawa kasar ta Kenya wajen kawo karshen matsalar tattalin arzikin su kamar yadda yayi a kasar Amurka.

“Ni ne mutumin da ya gyara harkar tattalin arzikin kasar Amurka a tarihi, ina ganin idan an bani dama zan iya taimakawa kasar Kenya.”

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan