Jihar Kano Ba Jihar Imo Ba Ce – Salihu Tanko Yakasai.

368

Tun bayan da kotun koli wato Supreme Court ta yanke hukuncin shariar zaben jihar Imo, inda ta kwace kujerar Gwamnan jihar daga hannun Ihedioha ta mika wa Ozodinma, yan Kwankwasiyya sun shiga tsalle da shewa suna tunanin wai hakan ce zata faru a Kano, a irin tasu haukar.

Ganin haka na ga dacewar nai fashin baki na hankali, ga masu hankalin cikin su, ko sa hankalta su gane cewa Shari’ar jihar Imo, ta sha banban da Shari’ar jihar Kano, bisa wannan dalilai da zan zaiyana.

A zaben jihar Imo dai, Jam’iyar APC ta kai karar cewa a wurin zabe da suka haura 380, ba’a saka sakamakon da Jam’iyar APC ta samu ba, wanda wannan ya bawa Jam’iyar PDP nasara, ta kuma kalubalanci wannan abu a kotu, inda har lamarin ya kai ga kotun koli.

Alkalan kotun koli sun yi nazari, sun duba ka’idojin zabe, suka gamsu cewa tabbas rashin saka sakamakon wuraren nan har fiye da waje 380 Wanda yawan kuri’un su ya haura dubu dari biyu, ba daidai bane kuma ya sabawa ka’idojin zabe. Nan take suka yanke hukunci akan a karbi wannan sakamako a tara da wanda PDP ta ce shine na zahiri kuma akai hakan wanda shine ya bawa Jam’iyar APC nasara.

Kwatankwacin iin wannan shine ya faru a Shari’ar zaben Hon Ado Alhassan Doguwa, inda shima kotu ta soke zaben saboda ba’a saka sakamakon da Jam’iyu fiye da 50 suka samu ba, sai na APC da PDP kawai aka saka, kuma wannan ya saba kaidojin zabe kuma kotun daukaka kara ta ce INEC tayi kuskure yin hakan wanda wannan shine ya janyo sake zaben Tudun Wada da Doguwa.

Amma a maganar zaben jihar Kano tsakanin Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR da Abba na PDP, yan Kwankwasiyya sun kai kara ne akan su basu yadda da zaben inconclusive ba, sun ce babu shi a tsarin mulki. Sai dai wannan yaudara ce da hauma hauma irin wadda yan Kwankwasiyya suka saba.

Domin kuwa ba’a jihar Kano kadai aka fara inconclusive ba, anyi na farko a jihar Kogi, sannan anyi a Jihar Osun, kuma duk gaba daya babu inda aka ce yin zaben inconclusive haramun ne.

Domin kundun tsarin mulki ya bawa hukumar zabe cikakken iko ta gudanar da zabe duk yadda taga ya dace domin a samu wanda yai nasara da wanda ya samu akasin haka.

Tun a kotun zabe a matakin jiha, mai Shari’a Halima Shamaki tai kaca-kaca da bukatar yan Kwankwasiyya akan neman a soke zaben.

Duk bukatun su gaba daya sai da ta tsefe su, ta fiffige su, kuma ta dagargaza su akan cewa ba su da hujja. Babban abun laakari da shi a nan shine, idan yan Kwankwasiyya basu yadda da inconclusive ba, toh mey ya sa suka shiga zaben?

Domin kowa ya san sun yi campaign, a ranar zabe sun tura agents din su, mutanan su sun fita sun zabe su, sannan sun tura wakilai lokacin da hukumar zabe ta INEC ta karbi sakamakon inconclusive sannan ta tabbatar da nasara ga Gwamna Ganduje.

Sai da aikin gama ya gama a Gama, shine kuma yan Kwankwasiyya zasu ce su basu yarda ba? Don sun sha ka yi? Wannan ai rainin hankali ne irin na wanda basu san abinda suke ba.

Yadda kotun zabe a matakin jiha ta kori karar yan Kwankwasiyya, haka ta daukaka kara a Kaduna ita ma tai watsi da karar su kuma kotun koli ma haka za tayi da yardar Allah.

Domin ita kotun koli bata karbar sabuwar hujja, aiki take da hujjojin da aka shigar a kotun zabe ta farko da kuma ta kotun daukaka kara, wanda dukkannin su, sun amince cewa Gwamna Ganduje ya yi nasarar lashe zaben sa.

Da wannan hujjoji nake kira ga magoya bayan Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR da Jam’iyar APC ta jiha da kasa baki daya, da su San cewa a ranar litinin 20 ga watan January, da Izinin Allah, nasara ta Gwamna Ganduje ce.

Babu wani dalili da abunda ya faru a Jihar Imo zai faru a Kano, domin kwata kwata hanyar jirgi da ban, ta mota da ban. Gwamna Ganduje zai musu 4-0 In Sha Allah kuma daganan sai Jana’izar Kwankwasiyya a Najeriya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan