Rashin Tsaro: An Kafa Dokar Taƙaita Zirga-Zirgar Babura A Katsina

315

A wani yunƙuri na shawo kan matsalar sace-sacen mutane da sauran matsalolin tsaro, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sa hannun kan wata doka da ta hana amfani da babura masu ƙafa biyu da masu ƙafa uku a faɗin jihar daga ƙarfe 7 na yamma zuwa 6 na safe daga ranar 20 ga Janairu, 2020.

Babban Lauyan Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar, Ahmed El-Marzuq ya sanar da haka ranar Laraba a Katsina.

“Sashi na 5, ƙaramin sashi na 2 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima ya ba gwamnan ikon sa hannu a wannan doka.

“Dokar ita ce Dokar Taƙaita Zirga-Zirgar Babura Masu Ƙafa Biyu da Masu Ƙafa Uku ta 2020. A ƙarƙashin wannan doka, ya haramta zirga-zirgar babura a dukkan faɗin jihar nan daga ƙarfe 7 na yamma zuwa 6 na safe, daga 20 ga Janairu, 2020.

“Dokar za ta yi aiki a kan kowa da kowa a jihar nan.

“Amma, akwai togaciya. Dokar ba za ta yi aiki a kan sojoji, ‘yan sanda da sauran jami’ai masu horo irin na soji ba kamar Jami’an Hukumar Kiyaye Afkuwar Haɗura ta Ƙasar, FRSC, Jamian ‘Civil Defense’, Jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice, NIS, Jami’an Hukumar Hana Fasa Ƙwauri, NCS da sauran hukumomin tsaro”, in ji shi.

Ya ce yana da muhimmanci kowa ya bi wannan doka, yana mai gargaɗin cewa masu kunnen ƙashi za su iya fuskantar zaman gidan yari na shekara ɗaya da zaɓin biyan tara ko kuma duk biyun, kamar yadda dokar Penal Code ta tanada.

Mista El-Marzuq ya ce an ɗauki wannan matakin ne don a kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

“Ana aikata mafiya yawan sace-sacen mutane ne da sauran muggan laifuka a waɗannan sa’o’i ta hanyar amfani da wannan hanyar sufuri.

“Ba a hana mutane zirga-zirga ba, za su iya amfani da motoci.

“Da zarar al’amura sun daidaita, za a sake duba dokar”, in ji Mista El-marzuq.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan