A ƙalla mutane 30 sun rasa rayukansu, inda kuma ake tsoron an yi garkuwa da mutum 100 bayan ‘yan bindiga sun buɗe wuta a kan masu wucewa kan Babbar Hanyar Kaduna-Zariya ranar Talata, a cewar wani rahoton tsaro da sanarwar ‘yan sanda.
Sarkin Potiskum, Umar Bubaram yana daga cikin waɗanda suka samu muggan raunuka, kuma har zuwa Laraba da daddare yana asibiti yana karɓar magani, a cewar ‘yan sanda.
‘Yan bindigar sun buɗe wuta ne a kan jerin gwanon motocin Sarki Bubaram a Maraban Jos da misalin ƙarfe 11:00 na dare, a cewar majiyoyin tsaro.
Jaridar PREMIUM TIMES ta bada rahoton cewa Sarkin ya rasa direbobinsa huɗu a harin.
Wata sanarwa da ta fito daga ‘yan sanda ranar Laraba ta ce maharan suna sanye da kakin soja lokacin da suka isa Maraban Jos ɗin, wajen da ya zama shahararren wajen da masu garkuwa da mutane ke cin karensu ba babbaka.
Mai Magana da Yawun Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kaduna, Sabo Abubakar ya ce mutum shida kawai aka kashe a harin, yayinda biyar suka samu raunuka.
Ya amince da cewa an yi garkuwa da mutane da dama, amma bai bada alƙaluma ba.
Sai dai manyan majiyoyin tsaro da aka tattauna da su kan faruwar al’amarin sun faɗa wa majiyarmu ta PREMIU TIMES cewa ana tsoron mutanen da suka mutu sun kai 30 a ranar Laraba da safe.
Wannan hari dai shi ne na baya-bayan nan a jerin hare-hare da ake kai wa farar hula a jihar Kaduna da jihohi maƙobta a Arewa Maso Gabashin Najeriya.
Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmed Lawan, wanda ɗan jihar Yobe ne, jihar da Potiskum ke ɗaya daga cikin manyan garuruwa ya mayar da martani ga harin cikin gaggawa, ya yi Allah-wadai da shi da kakkausan lafazi, ya kuma yi wa waɗanda harin ya shafa jaje.
‘Yan sanda su ce tuni sun fara bincike don cafke waɗanda ake zargin ranar Laraba.
[…] Muƙalar Da Ta GabataSarkin Potiskum Ya Sha Da Ƙyar A Hannun Mahara […]