Wata Baturiya Daga Ƙasar Amurka Ta Biyo Saurayinta Zuwa Kano

2326

Wata ba amurkiya da ke zaune a birnin Carlifonia tayo tattaki daga Amurkan bata zame ko in aba sai a unguwar Panshekara dake nan Kano, tazo takanas ta Kano domin ganawa da wani saurayin ta, dan Kano mazaunin Panshekara wanda su ka kulla abota a dandalin sada zumunta daga bisani kuma abin ya zama soyayya me karfi har takai guda baya iya runtsawa sai ya ji muryar gudan.

Baturiyar mai suna Janet ta yanki tikiti ta hawo jirgi ta sauka a jihar Kano, inda daga nan ne ta garzaya unguwar Panshekara, ta kuma shiga har cikin gidansu wannan saurayi na ta Suleman wanda ta ce ya gama sace zuciyar ta da kalamai na soyayya da hotunan ƙawa da ya ke tura mata cikin yanayin rangwada.


Janet ta bayyana cewa kuma ta shirya tsaf domin ɗaukar wannan saurayi na ta domin tafiya dashi can ƙasar Amurka a cigaba da shan soyayya.

A nasa ɓangaren Suleman ya ce shima fa ya yi mata kuma kayansa su na jaka zai bi matar ta sa amma ya yi alkwarin zai dinga kawo ziyara gida.

Ita kuwa Fatima Suleman mahaifiyar wannan saurayi da makota ke yiwa barka ta ce, bata da suka a kan wananan alaka domin haka a tafi Amurka ta amince.

Sai dai kuma wani abu da ke jan hankali al’umma shi ne ita fa wannan ba Amurkiya shekarar ta 46 shi kuwa Suleman yaro n mai shekaru 23,

Freedom Radio Kano

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan