Yadda Aka Damfare Ni Sama Da Naira Miliyan 60 – Bashir Ɗalhatu

250

Tsohon Ministan Makamashi da Karafa, Bashir Dalhatu, ya bayyana wa Mai Shari’a yadda wani mutum mai suna Imeh Akpan ya damfare shi kudi har naira milyan 68.9.

Ya bayyana wa Mai Shari’a na Babbar Kotun Zuba, a Abuja cewa cikin 2004 ne wasu abokan sa su biyu, suka hada shi da Akpan.

Dalhatu ya ce Akpan ya shawarce shi da ya bada kudi a kafa kamfanin zirga-zirgar jiragen sama. Ya ce masa akwai riba sosai a harkar.

Dalhatu ya amince ya sayi hannun jari na naira milyan 1.8, wanda ke daidai da kashi 34% na adadin hannayen jarin kamfanin.

“Akpan daga baya ya ce min ya yi kokarin karbar ramce a First Atlantic Bank, amma bai samu ba. Don haka ya na so na kara zuba naira milyan 50.

“Ranar 28 Ga Maris na ba shi cakin kudi na naira milyan 58. Daga baya kuma na kara masa naira milyan 10.7.”

Dalhatu ya shaida wa kotu cewa da ya ga abin ya koma damfara, ya nemi kudin sa, amma bai samu ba.

Cikin 2013 ne Dalhatu ya kai korafi a Hukumar EFCC domin a neman masa hakkin sa.

An dage shari’ar zuwa ranar 2 Ga Maris, domin ci gaba da saurare.

Lauyan Akpan ya nemi beli, kuma Mai Shari’a ya amince, aka bada belin sa.

Premium Times

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan