Home / Siyasa / Ina Kyautata Zaton Ganduje Zai Sha Ƙasa A Kotun Ƙoli – Buba Galadima

Ina Kyautata Zaton Ganduje Zai Sha Ƙasa A Kotun Ƙoli – Buba Galadima

Tsohon jigo a jam’iyyar CPC kuma tsohon aminin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Buba Galadima, ya bayyana hukuncin kotun koli wacce ta kaddamar da Hope Uzodinma zababben gwamnan jihar Imo a matsayin babbar almara a tarihin duniya.

Ya ce: “Abunda ya faru shi ne cewa kotun koli a yanzu ta daure kanta saboda ta yaya za su yiwa Emeka Ihedioha haka sannan su ki yiwa Abba Kabiru Yusuf a Kano? Iri abu guda sak ne ya faru a Kano.

“Idan har ya zama dole a soke zabe, ya kamata ya kasance a matakin rumfar zabe ya kamata a soke a cewar kotun koli.

Amma a Kano, ba a soke kuri’un a wajen zabe ba; ba a soke su a matakin unguwa ba sai dai an soke su ne a matakin karamar hukuma.

Don haka idan har ba a ce Ganduje ya tafi ba sannan aka fadi wani abu sabanin haka, lallai Najeriya za ta ga tashin hankali.”

Hukumar zabe mai zaman kanta a halin da ake ciki, ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga Uzodinma a ranar Laraba.

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Ni da Obasanjo mu ka kuɓutar da ɗaliban babbar kwalejin gandun daji ta Afaka – Sheikh Gumi

Fitaccen malami Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana rawar da shi da Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *