Wani Mutum Zai Yi Zaman Gidan Yari Na Makonni Biyu Sakamakon Amsa Waya A Kotu

303

Mai Shari’a Sikiru Oyinloye na Babbar Kotun Jihar Kwara ya yanke wa wani mutum, Abdulwahab Adebayo hukuncin zaman gidan gyaran hali na makonni biyu saboda amsa waya da ya yi a yayin zaman kotun.

Mista Adebayo ya je kotun ne don sauraren wata shar’ia, sai ya yi ta ɗaga waya.

Mai Shari’a Oyinloye ya ce Mista Adebayo ya kawo wa kotun cikas, kuma lokacin da jami’in ɗan sanda da ke aiki a kotun ya kira shi da ya daina ɗaukar hankalin kotun, sai ya ƙi.

Alƙalin kotun ya samu Mista Oyinloye da laifin kawo cikas ga zaman kotun da hirarsa ta waya.

“Mai laifin ya ƙi ya daina ɗaukar hankalin kotun har sai da wani ɗan sandan ya fitar da shi waje.

“Ya kuma nuna halin rashin ɗa’a a kotun saboda yadda ya riƙa yin ihu yana cewa shi ba shi da laifi.

“Kotu ba wajen yin kiran waya ba ne na kuɗi inda kowa zai iya karɓar kira ko ya yi kira yadda ya ga dama.

“Mutane sukan aikata laifin raina kotu da raini. Jahiltar doka laifi ne. Saboda na yanke maka hukuncin zaman gidan yari na mako biyu, ba tare da zaɓin biyan tara ba”, Mai Shari’a Oyinloye ya yanke hukuncin haka.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan