Ina Matan Kannywood Ke Samun Kuɗin Da Su Ke Zarya A Ƙasashen Waje?

314

DUK mai bibiyar harkokin finafinan Hausa ya san mugun yanayin da masana’antar Kannywood ta ke ciki. Saboda kasuwar ta karye, ba kowa ke yin fim ba. Shirya fim ya koma sai jefi-jefi, sannan kusan duk finafinan da ake yi an fi saka ƙananan jarumai mata kuma sababbi, domin sun fi araha.


Hakan ya sa yawancin ’yan fim sun rasa abin yi, sai kame-kame. Masu ɗan ƙarfin cikin su kuma sun kama wasu sana’o’in don samun abin sakawa a bakin salati. Wasu masu ɗan ƙarfin, musamman mata, sun kama kasuwanci.


To amma a yayin da masana’antar ta ke cikin wannan hali na ha’ula’i, shugabanni sun gaza samun mafita, mujallar Fim ta lura da yadda wasu fitattun jarumai mata ɗaiɗaiku su ke fantamawa ta hanyar yawan fita ƙasashen ƙetare, su na holewa abin su.

Su na nuna halin ko-in-kula da halin da masana’antar ta ke ciki.


Da ma ‘yan fim kan fita waje, to amma yanzu sun ƙaru. Tun a farkon shekarar 2019 jaruman su ke ta karakainar zuwa ayyukan Umra da Hajji; wasu zuwan su na farko ne, wasu kuma kusan duk shekara sai sun tafi. Sannan kuma sai masu zuwa London, Paris, Dubai, Cyprus da wasu ƙasashe da su ka haɗa da Amerika da Indiya. Abin ya zama kamar gasa.


A ƙarshen shekarar nan ta 2019 da ta gabata, wasu ɗaiɗaikun jarumai mata su ka fara barin Nijeriya su na keta hazo zuwa ƙasashen ƙetare domin hutu da yawon buɗe ido, wasu kuma sayayya. Wasu daga cikin matan Kannywood da su ka fita waje a 2019 su ne:

Hadiza Gabon a Rome

Fati Washa, Hadiza Gabon da Rahama Sadau sun je London bikin gasar finafinai inda aka ba Washa awad. Wannan shi ne zuwan Washa ƙasar Ingila na farko, su kuwa su Rahama da Gabon sun saba zuwa, don ita Rahama fita waje ya zamar mata kamar daga Kaduna ta tafi Abuja ko Kano.

 1. Yaseera B. Yola ta tafi Dubai, daga can ta wuce Addis Ababa a ƙasar Ethiopia.
 2. Amal Umar ta je Umrah a Saudiyya, daga can ta tafi Dubai.
 3. A lokuta daban-daban, Hadiza Gabon ta je Spain da Italiya da London da Paris da Dubai.
 4. Maryam Isah Abubakar (Ceeteer), ƙanwar Mansurah Isah ta je aikin Umrah, daga can ta wuce Dubai.
 5. Fati KK ta je Dubai.
 6. Sadiya Kabala ta je aikin Umrah, daga can ta wuce Dubai.
 7. Aisha Ahmad Idris (Ayshatulhumaira) ta je Dubai.
 8. Sapna Aliyu Maru ta je aikin Umrah, daga can ta tafi Dubai.
 9. Fati Washa ta je Dubai, inda su ka haɗe da Hadiza Gabon.
 10. A lokuta mabambanta, Rahama Sadau ta je Cyprus da Masar da Paris.
 11. A lokuta daban-daban, Nafisat Abdullahi ta tafi yawon buɗe ido a New York a Amurka da kuma London inda ta yi zaman ta kamar ba za ta dawo ba.
 12. Fati Nijar ta je Paris inda aka naɗa ta Gimbiyar Sarkin Hausawan Nahiyar Turai.

Ba a maganar waɗanda su ka je aikin Hajji, waɗanda su na da ɗan dama, wato irin su Hafsat Idris, Maryam Yahya, Ruƙayya Dawayya, da sauran su.


A ‘yan fim maza, in ban da Jamilu Ahmad Yakasai (mai yawan zuwa London) da Ali Nuhu, da wuya a kawo ƙarin sunayen mutum biyu da su ka hau jirgin sama su ka je wata ƙasa in ba aikin Hajji ba.

Wani abu shi ne duk inda waɗannan jarumai mata su ka je, bai ɓoyuwa; za a gan su su na ɗaukar hotuna na nuna isa, su na turawa a shafukan su na soshiyal midiya.

Duk da yake wasu masoyan ‘yan fim na ganin cewa ci-gaba ne a ga ’yan fim ɗin Hausa sun kai matsayin da za su riƙa fita yawon shaƙatawa a ƙasashen duniya, yawan fitar tasu ya haifar da tambayoyi a zukatan jama’a.

Tambayoyin sun haɗa da: Shin su waɗannan mata halin da masana’antar ke ciki bai shafe su ba ne? A ina su ke samun maƙudan kuɗaɗen da su ke kashewa wajen neman biza da hawa jirgi su tafi wata ƙasa, su kama otal a can, su ci abinci, su yi yawon buɗe ido, su yi sayayya? Yawancin su dai (in ban da kamar Sapna Aliyu Maru) ba wata sana’a mai ƙarfi su ke da ita ba inda su ke samun ribar da ta isa su tafi yawo wata ƙasa. Su kuma ba bisa gayyatar zuwa wani taro su ke waɗannan tafiye-tafiyen ba.

Sannan me ya sa wasu tsirarun matan Kannywood ne kaɗai su ke wannan fantamawar yayin da mazan su ke fama da fatara?


Wani babban furodusa wanda ya ke so mu sakaya sunan sa ya faɗa wa mujallar Fim cewa: “Bari in gaya maka gaskiya, waɗannan ‘yan matan duk a wajen maza su ke samun kuɗaɗen da su ke waɗannan tafiye-tafiyen.


“Ka duba mana, nawa mutum zai kashe ya tafi Paris ko Dubai? Aƙalla ka nemi miliyan ɗaya. To tafiyar da wata jarumar ke yi za ta kashe sama da naira miliyan ɗaya da rabi. A gidan uwar wa ta samo kuɗin?”


Ya ƙara da cewa, “Ban ce dukkan su ba, amma kashi casa’in da tara cikin ɗari ba a harkar fim su ke samun wannan kuɗin ba. Fim ake yi ana biyan su? Kuma nawa ake biyan nasu a fim ɗin? Yaushe rabon da ka ga wata cikin waɗannan jaruman a lokeshin? Sannan masu shago a cikin su mutum nawa ne?


“Kuma ka kula, ko a nan Najeriya ɗin dubi irin facakar da su ke yi da kuɗi. Har gidaje su ke ginawa, ga manyan motoci, ga tsadaddun tufafi da manyan wayoyi. Ba a ma maganar kayan shafe-shafen su da abincin da su ke ci.

Sannan wasun su su ne ke ɗaukar nauyin iyayen su. Kuma su kan bada kyauta ga ‘yan’uwa da mabuƙata. Kai ka san sai maza sun ba su!”


Ya ce duk industiri an san inda matan ke samun kuɗin da su ke wannan zirga-zirgar.

Wani ɗan fim kuma ya yi tambayar me zai sa waɗannan matan masu fantamawa ba za su yi tunanin yadda za a gyara harkar fim ɗin ba, ta dawo yadda ta ke? Me zai hana ‘yan fim mata su yi ƙungiya su nemi haɗin gwiwar manyan jarumai da furodusoshi irin Ali Nuhu, Adam A. Zango, Falalu Ɗorayi, Abubakar Bashir Maishadda da shugabannin su na MOPPAN don ganin an ceto Kannywood daga halin da ta ke ciki?


Kwanan nan wani wakilin mujallar Fim ya ziyarci wata fitacciyar jaruma, sai su ke zantawa game da halin da Kannywood ta ke ciki. Sai ta ce masa, “Yanzu da za a iya haɗa kai, a ce Ali Nuhu, Adam A. Zango da Hadiza Gabon kawai su na da ƙarfin da za su iya canza akalar masana’antar nan ta yadda za a samu ci-gaba, amma ba za a yi ba.”


Mutane da yawa da ke bibiyar hotunan su na yin Allah-wadai da yadda ‘yan fim ɗin su ke nuna yadda su ke shaƙatawa abin su. A cewar su, hakan babu abin da zai haifar sai zubar da ƙimar su, don haka ya kamata a ce sun zama jakadu nagari.


Mujallar Fim ta nemi jin ta bakin wasu daga cikin ‘yan fim ɗin, musamman ma waɗanda ake maganar a kan su, amma da yawan su sun ƙi yin magana a kai. Sai Sapna Aliyu Maru ce ta ce wani abu, inda ta ce, “To ni da man ina zuwa Dubai ina sayo kaya tsawon lokaci, don haka ba wani abu ba ne sabo a gare ni.


“Kasuwanci ne ya ke kai ni, don haka ba yawon shaƙatawa ko tallar kai na na je ba. Kuma ko da na yi tallar kai na ai ni budurwa ce, don haka ba wani abu ba ne.

Nafisat Abdullahi a New York

“Abin ma da ya sa aka ga haka a wannan lokacin, saboda zuwan namu ya zo daidai da hutun ƙarshen shekara da shiga sabuwar shekara, don haka ba mu kaɗai ba ne; duk masu zuwa ma haka su ka yi.”


Wata ‘yar fim da ta saba zuwa Dubai wadda ta buƙaci a ɓoye sunan ta kuwa cewa ta yi, “Kai rabu da su kawai! Sun je dai su yi abin da ya kai su ne dai, domin wasu idan kasuwanci ne ya kai su, wasu kuma samarin su ne su ka kai su, don haka kai dai a yi sha’ani dai kawai.


“Mu da mu ke zuwa Dubai ɗin ka gan mu mu na nuna kan mu? Sayen kaya ya kai mu kuma shi mu ke yi, sai mu je mu dawo ma ba tare da kowa ya sani ba.”

Game nuna ba ruwan su da taimakawa don a tsamo harkar faga cikin mugun yanayi, wani ɗan fim ya faɗa wa mujallar Fim cewa: “Kada su ga cewa ai su yanzu duniya ta san su, masana’antar ba ta da sauran amfani a wurin su don sun riga sun samu abin da su ke so.


“Idan su ka yi duba da kyau, jaruman baya ba su samu irin wannan damar ba, kuma su ma sun yi tashe fiye da jaruman yanzu.


“Idan kuwa har su ba za su haɗa kan su don ganin an ceto masana’antar nan daga halin da ake ciki ba, to an samu ci-gaban mai haƙar rijiya kenan.”

Nafisat Abdullahi a birnin Las Vegas na ƙasar Amurka
Fati KK a Dubai
Yaseera B. Yola a Ethiopia
Rahama Sadau a Paris

Daga Fim Magazine

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan