Wasu Aladu Sun Kashe Ubangidansu Tare Da Cinye Shi

330

Waɗannan aladu sun cinye wani manomi bayan ya fadi a cikin dakinsu sanadiyyar bugun zuciya.

Manomin mai shekaru 71 a duniya, wanda aka bayyana sunanshi da Mr Krzysztof, yaje ya debo ruwa a cikin wata rijiya dake cikin gonarshi dake kauyen Osiek, a yankin Kudu Maso Yammacin kasar Poland.

Yana cikin gonar kawai sai ya fadi sanadiyyar bugun zuciya, nan take aladun nashi guda goma sha biyu suka fara cin naman jikinshi.

Wani makwabcinsa ne ya gano kasusuwanshi a lokacin da yake yawo a yankin wajen bayan shafe tsawon lokaci basu ganshi ba.

A lokacin da makwabcin nashi ya isa wajen yaga kokon kanshi da kuma wasu kasusuwa na sassan jikin mutum a yashe a wajen.

A cewar makwacin, Mr Krzysztof na da matsalar shaye-shaye, kuma yana iya yiwuwa ya fara bacci ne a lokacin da yaje rijiyar domin debo ruwan.

Haka kuma hukumomi sun bayyana cewa zai iya yiwuwa ya gamu da bugun zuciya ne a wajen.

Wani makwabcinsa kuma cewa yayi: “Zai iya yiwuwa ya manta ya bawa aladun abinci ne kuma bacci ya dauke shi a wajensu.” inji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan