Ku Daina Kiran Mu NEPA Idan Kuna Son Wuta- DisCos

235

Sunday Oduntan, Babban Daraktan Bincike da Wayar da Kan Jama’a na Ƙungiyar Masu Rarraba Wutar Lantarki ta Ƙasa, ANED, ya roƙi ‘yan Najeriya da su daina kiran ‘yan ƙungiyar NEPA.

ANED ƙungiya ce dake ƙarƙashin Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki, DisCos.

Da yake jawabi a wani shiri a gidan talabijin na TVC, Mista Oduntan ya ce idan ‘yan Najeriya suka ci gaba da kiran su NEPA, hakan na nufin ba sa son wutar lantarki.

A da, Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Ƙasa, NEPA, ita ke da haƙƙin samar da wutar lantarki, tunkuɗo ta da rarraba ta a Najeriya, amma daga bisani aka canza mata suna zuwa Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Najeriya, PHCN.

“Na fahimci yadda ‘yan Najeriya ke ji idan aka ce su biya kuɗi da yawa don siyan wani abu. Amma, muna so ‘yan Najeriya su fahimci waɗannan abubuwa masu zuwa: Na ɗaya, ku daina kiran mu NEPA”, in ji Mista Oduntan.

“Kuna ci gaba da kiran mu NEPA, hakan yana nuna cewa ba ku san abu ya sauya ba a ƙasar nan. Yana nufin ba kwa son wani canji. Yana nufin ba ma kwa son wutar lantarki. Ni haka nake ganin abin.

“Mu DisCos ne, amma ba ma taka rawar DisCos. Mu kamfanonin rarraba wutar lantarki ne. PHCN ya mutu, NEPA ta mutu.

Da yake magana kan ƙarin kuɗin wutar lantarki da Hukumar Kula da Samar da Wutar Lantarki ta Ƙasa, NERC ke shirin yi, Mista Oduntan ya ce wasu dalilai ne suka kawo za a yi ƙarin kuɗin.

“Fiye da kaso 95% na kayayyakin da muke amfani da su a ɓangaren wutar lantarki shigo da su ake yi”, in ji shi.

“A yanzu, dole su duba canjin kuɗaɗen ƙasashen waje, tashin farashin kaya. Sai sun duba kuɗin samar da wuta, har da kuɗin gas. Idan duk waɗannan abubuwa suka yi ƙasa, kuɗin wutar ma zai yi ƙasa”, ya ƙara da haka.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan