Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya yaba wa alƙalan Kotun Ƙoli bisa nasarar da ya yi, yana mai kira ga abokan hamayya da su haɗa kai da shi don ciyar da jihar Kano gaba.
Idan dai ba a manta ba, a yau Litinin ne Kotun Ƙolin ta tabbatar da zaɓen Gwamna Ganduje na jam’iyyar APC, bayan da ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar PDP da ɗan takararta, Abba Kabir-Yusuf suka ɗaukaka a gabanta.
A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran gwamnan,, Abba Anwar ya fitar, Gwamna Ganduje ya bayyana godiyarsa ga Allah da al’ummar jihar Kano bisa yadda suka “gudanar da al’amuransu cikin lumana” a jihar.
“Mun gode wa Allah bisa wannan nasara da Kotun Ƙoli ta tabbatar mana bayan hukunce-hukuncen Kotun Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Zaɓe da na Kotun Ɗaukaka Ƙara.
“Muna kuma gode wa al’ummar jihar Kano bisa yadda suka gudanar da al’amuransu cikin lumana”, Mista Anwar ya jiyo gwamnan yana faɗin haka.
Mista Anwar ya ƙara da cewa gwamnan ya kuma gode wa dukkan mutanen da suka yi addu’a tuƙuru wadda ta tabbatar da nasararsa, yana mai jaddada cewa: “Duk wanda ya yi imani kuma ya dogara da Allah, a kodayaushe zai yi nasara a farko, tsakiya da ƙarshen al’amari, duk yadda aka je aka komo”.
“Muna kuma yaba wa dukkan alƙalai da suka taka rawa a wannan aiki na zurfafa dimokuraɗiyya. Wannan ya nuna jajircewar alƙalanmu wajen ƙarfafa dimokuraɗiyyarmu”, in ji shi.
“Ina jaddada cewa ya kamata abokan hamayyarmu su zo su haɗu da mu don ciyar da jihar nan gaba. Muna da ayyukan raya ƙasa da yawa a ƙasa. Kuma wasu suna zuwa.
“Manufarmu ta ilimi kyauta kuma dole tana buƙatar haɗin kan kowa. Haka ma tsarin tsaronmu yana buƙatar tallafin kowa. Da abubuwa da yawa”, a kalaman Mista Anwar.
“Jim kaɗan bayan sanar da hukuncin Kotun Ƙoli, Gidan Gwamnati ya cika da jama’a masu murnar wannan nasara. Irin waɗannan mutane sun kuma bazu a titunan Kano”, sanarwar ta lura da haka.
[…] Muƙalar Da Ta GabataHukuncin Kotun Ƙoli: Ganduje Ya Gayyaci Abba Ya Zo Su Yi Aiki Tare […]