Shahararriyar ‘yar wasan Tennis dinnan ta duniya kuma ‘yar kasar Amurka wato Serena Williams ta fara gasar Australian Open da kafar dama.
Inda Serena ta lallasa Anastasia Potapova daci 6 – 0 dakuma 6 – 2 tun adaidai mintina na 58.
Wannan shine karo na 19 da Serena Williams take halartar gasar Australian Open kuma ta lashe gasar sau 7 atarihi.

Wannan gasa ta Australian Open tana daga cikin gasoshi manya a duniyar Tennis wadanda akayiwa lakabi da gasa mai daraja ta farko wato Grand Slams.
Turawa Abokai
[…] Muƙalar Da Ta GabataSerena Williams Tafara Gasar Australian Open da Nasara […]