Sinadarin Haɗa Shayi Ya Haddasa Asarar Rayuka A Kano

225

Tsohon daraktan ma’ikatan jinya a asibitin kwararru na Murtala Muhammad a jihar Kano, Yusuf Yakubu, ya ja hankalin al’umma da su kauracewa yin amfani da kayayyakin da wa’adin su ya kare wato dameji.

Jami’in lafiyar ya bayyana hakan ne, lokacin da ya ke tsokaci tare da bayyana alhinin sa a kan yadda ake zargin kananan ‘ya’yansa sun sha wani sinadarin hada shayi kalar makuba wanda ake amfani da shi a shayi yau da kullum.

Yusuf Yakubu, ya ce “ Ta sanadiyar shan sinadarin suka rasa ransu wanda wa’adin amfani da shi yak are, kuma suna shan garin cikin su ya rinka kadawa su hudu a lokacin. Mun yi kokarin kai su asibiti biyu sun mutu daga cikin su”.

A ƙarshe masanin lafiyar ya kuma shawarci mahukunta da su kara kaimai wajen dakile samuwar irin wadannan kayayyaki a kasuwanni.

Freedom Radio, Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan