Home / Lafiya / Ana Fargabar Ɓullar Zazzaɓin Lassa A Kano

Ana Fargabar Ɓullar Zazzaɓin Lassa A Kano

Rahotanni daga Kano na cewa ana fargabar barkewar annobar zazzabin Lassa a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.

An fara zargin cewa annobar ta barke ne a asibitin bayan likitocin da suka duba wani mara lafiya sun mutu, sannan wasu mutum uku da suka yi mu’amala da shi yanzu haka na kwance cikin halin jinya.

Mara lafiyar dai ya je asibitin ne daga jihar Bauchi.

Kawo yanzu dai ba a tabbatar da cewa ko zazzabin na Lassa ne ya barke ba, sai dai wani likita a asibitin ya shaida wa BBC cewa alamu na nuna annobar Lasa ce ta barke a asibitin.

Wata majiyar kuma ta shaida wa BBC cewa an dauki jinin mutanen da suka yi mu’amala da mara lafiyar da kuma likitocin da suka mutu, kuma yanzu haka ana tantance jinin a dakin bincike.

Zuwa karfe uku na yammacin Talatar nan ne ake sa ran hukumomin asibitin za su fitar da sanarwa a kan batun.

BBC Hausa

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Ƙudurin samar da Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya a Rano ya tsallake karatu na biyu

A yau Laraba majalisar wakilai ta ƙasa ta amince da karatu na biyu kan dokar …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *