Duk Waɗanda Su Ka Zaluncemu Allah Ya Tsine Musu Albarka – Sanata Kwankwaso

186

Tsohon gwamnan jihar Kano, madugun darikar siyasar Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya mayar da martani game da hukuncin kotun koli game da zaben gwamnan jihar Kano, inda ya fara da tofin Allah tsine.

Wannan shi ne karo na farko da aka jiyo madugun Kwankwasiyya yace wani abu game da hukuncin kotun kolin, inda aka jiyo shi cikin wani bidiyo yana tsinuwa ga duk wadanda suka sa hannu cikin zaluntarsa, kamar yadda shafin Dokin Karfe ya dauko bidiyon.

“Kana shan tsinuwa, ko mutum ba’a tsine masa ba, ballantana kullum muna cikin tsine masa, ko yanzu ma ina cewa duk wa’anda suka zalunce mu dana gida, dana waje Allah Ya tsine musu albarka.” Sai jama’ar dake wajen suka dauka da “Amin”

Kwankwaso ya cigaba da fadin; “Domin sun mana zalunci, sun zalunci mutan Kano, kuma zamu cigaba da tsine musu albarka damu da yayanmu da jikokinmu daga nan har abada. Sun lalata dimukradiyya, sun shiga cikin harkar sharia sun lalata ta.”

Idan za’a iya tunawa dai a ranar Litinin, 20 ga watan Janairu ne ma shairia Sylvester Nguta na kotun koli ya sanar da hukuncin koli game karar da dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jahar Kano, Abba Yusuf ya shigar da Gwamna Ganduje.

Da yake yanke hukuncin, Nguta ya bayyana karar da Abba da PDP suka shigar a matsayin mara tushe balle makama, don haka ya bayyana Ganduje a matsayin halastacce kuma zababben gwamnan jihar Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan