Hukuncin Kotun Ƙoli: Da Mun Rasa Kano Da Mun Yi Babbar Asara- Buhari

175

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya gwamman jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje murnar nasarar da ya yi a Kotun Ƙoli, wadda ta tabbatar da shi a matsayin halattaccen gwamnan jihar Kano.

Shugaba Buhari, wanda ya yi magana ranar Litinin ta bankin Mai Magana da Yawunsa, Garba Shehu, ya ce da sun rasa Kano a Kotun Ƙoli da hakan ya zama babbar asara ga jam’iyyar APC mai mulki.

Labarai24 ta kawo rahoton yadda Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar PDP da ɗan takararta na gwamnan jihar Kano a zaɓen gwamna na 2019, Abba Kabir-Yusuf suka ɗaukaka gabanta, a wani hukunci da gaba ɗaya gungun alƙan Kotun Ƙolin su bakwai suka amince da shi.

Shugaban Ƙasar ya kuma taya sauran gwamnonin APC murna, waɗanda Kotun Ƙolin ta tabbatar da zaɓe su, da suka haɗa da gwamnan jihar Filato, Simon Lalong.

“Na yi farin ciki yadda wannan gwagwarmayar shar’ia ta zo ƙarshe, jam’iyyarmu da gwamnoninmu suka yi nasara. Da mun yi babbar asara da a ce mun rasa jihohi masu muhimmanci, kamar Kano da Filato”, aka jiyo Shugaba Buhari yana faɗar haka.

Shugaba Buhari ya kuma taya “Majalisar Zartarwa ta Ƙasa ta Jam’iyyar APC murna, Kwamitin Zartarwa na Kasa na APC, da kuma dukkan ‘yan jam’iyya waɗanda jajircewarsu da biyayyarsu suka haifar da wannan nasara, musamman jihohi masu muhimmanci a siyasance kamar, Kano da Filato, bayan zafafan ƙalubalen shari’u”.

Amma Shugaba Buhari ya soki abokan hamayya waɗanda suka yanke hukuncin ƙalubalantar faɗuwar da suka yi a kotuna.

“A halin yanzu, ya zama tabbatacciyar ƙa’ida ga jam’iyyar hamayya ta ƙalubalanci duk wani zaɓe ko hukunci da bai ba ‘yan takararta nasara ba.

“Zaɓe ya yi kyau idan sun yi nasara. Zaɓe bai yi kyau ba idan wani ya yi nasara. Amma ba haka abin yake ba. Dimokuraɗiyya ba kawai ana maganar wanda ya yi nasara ba ne ko wanda ya faɗi, amma ana magana ne game da tsarin. A ƙoƙarin ƙalubalantar duk sakamako ko hukunci da bai yi musu daɗi ba, sai su ƙalubalanci tsarin gaba ɗaya”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan