Na Yafewa Kwankwaso Da Sauran Masu Ƙalubalantar Nasarata – Ganduje

481

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ya yafewa babban abokin adawarsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da kuma sauran masu kalubalantar shi a kotun koli.

A jiya Litinin ne kotun kolin tayi watsi da karar da dan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar PDP, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya shigar.

Da yake magana da manema labarai a gidan gwamnatin jihar, Ganduje ya ce yanzu lokaci yayi da za a ajiye banbancin akida da jam’iyya kowa yazo domin a ciyar da jihar gaba.

Yace adawa ta siyasa na ko’ina a duniya, amma idan jam’iyya daya ta samu nasara kamata yayi dayar ta goya mata baya domin kawo cigaba ga al’ummar yankin.

“Adawar siyasa gaskiya ce, ko a kasar Amurka jam’iyyu na irin wannan adawar a tsakaninsu.

“Amma mu a wannan karon tunda kotu ta bamu nasara, yanzu lokaci ne kuma da za a hada kai a yiwa jiha aiki.

“Na yafewa kowa da kowa, kuma ina fatan nima zaku yafe mini. Hatta ‘yan Kwankwasiyya na yafe musu, kuma ina kira gare su dasu zo mu hada karfi da karfe muyi aiki tare,” inji Ganduje.

Ganduje ya bayyana cewa ba zai taba saurarawa ba har sai ya sauke nauyin da ‘yan Kano suka dora masa a kanshi, “zamu kawo sabon tsarin tsaro a jihar nan. Mutanen Kano sun cancanci tsaro, saboda haka ina kira ga kowa da kowa su bamu hadin kai wajen gabatar da ayyukan mu.”

A karshe gwamnan ya mika godiyarshi ga Sarakuna guda biyar na jihar Kano, sannan ya godewa al’ummar jihar da dukkanin wadanda suka bashi goyon baya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan