Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Kano, Rabi’u Sulaiman Bichi, ya yi watsi da tsohon abokinsa a siyasance, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya koma jam’iyyar APC.
Jaridar DAILY NIGERIA ta ruwaito cewa Mista Bichi, wanda ya yi Sakataren Gwamnatin Jihar Kano daga 2011 zuwa 2016, zai sanar da matakinsa da na magoya bayansa na komawa jam’iyyar APC ranar Laraba da rana.
Majiyoyi da suke kusa da Shugaban Jam’iyyar sun ce ya ɗauki matakin barin jam’iyyar ne tun kafin Kotun Ƙoli ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan Kano, hukuncin da ya tabbatar da Abdullahi Umar Ganduje a matsayin halattaccen gwamna.
“Hukuncin Rabi’u Sulaiman Bichi ba shi da alaƙa da hukuncin Kotun Ƙoli. Ya ɗauki matakin ne bisa aƙidu da dalilan ƙashin kai”, a cewar wani abokin siyasarsa na kusa, wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa.
“A al’amuran Kwankwasiyya, an mayar da Rabi’u ba shi da amfani, an mayar da shi saniyar ware daga yanke hukunce-hukunce a Kwankwasiyya. Duk da jajircewarsa a tafiyar, ana yi masa kallon mai yin ƙafar angulu”, in ji majiyar.
Wannan ita ce ɓaraka ta baya-bayan nan a ɗariƙar Kwankwasiyya tun lokacin da tsohon mataimakin gwamna, Farfesa Hafiz Abubakar, tsohon Manajan Darkatan Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa, NPA, Aminu Dabo da sauransu suka bar tafiyar dab da zaɓukan 2019.