Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Ɓarkewar Zazzaɓin Lassa

222

A ranar Laraba ne gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutum uku sakamakon ɓarkewar Zazzaɓin Lassa a jihar.

Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya faɗa wa manema labarai a Ma’aikatan Lafiya ta Jihar Kano cewa an samu mutuwar mutum ukun ne a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.

A ta bakin Dakta Tsayawa, Ɗakin Gwaje-gwajen Cututtuka na Gaduwa Reference Laboratory dake Abuja ya faɗa wa Ma’aikatar Lafiya ta Kano cewa an samu mutum biyu da suka kamu da Zazzaɓin Lassa a Kano.

“Labarin farko shi ne na wata mata mai juna biyu ‘yar shekara 28 daga ƙaramar hukumar Gwale ta jihar bayan mahaifiyarta ta rasu, wadda aka kawo ta Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano daga wani asibiti mai zaman kansa ranar 31 ga Disamba, 2019, ta rasu ranar 1 ga Janairu, 2020. Ƙwararrun ma’aikatan lafiya sun bada kulawa ga wannan cuta ta farko, har ma da mutuwa biyu da aka tabbatar a asibitin, abinda ke jawo wa jihar ƙarin haɗari”, in ji kwamishinan.

Sai dai kwamishinan ya ce tuni gwamnatin jihar Kano ta ɗauki matakan shawo kan yaɗuwar cutar, yana mai ƙarawa da cewa za a ci gaba da sa ido a kan Zazzaɓin Lassa a dukkan faɗin jihar.

“Mun ɗauki matakan shawo kan yaɗuwar wannan cutar ta hanyar farfaɗo da Cibiyar Killacewa ta ‘Yar Gaya, farfaɗo da Tawagar Bada Agajin Gaggawa, gudanar da taron tattaunawa na Kwamitin Shirin Ko-ta-kwana”, in ji shi.

“A ƙoƙarin shawo kan yaɗuwar ɓarkewar cutar, ana ci gaba da wayar da kan ma’aikatan kula da lafiya kan Zazzaɓin Lassa, yadda ake gane shi da kamuwa da shi, riga-kafi da matakin kariya a cikin jihar nan, ma’aikatata ta ɗauki gabaren wayar da kan jama’a game cutar ta hanyar tallace-tallace”, ya ƙara da haka.

Sai dai kwamishinan ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da su riƙa ajiye abinci da ruwan sha a abubuwan da ɓera ba zai iya lalatawa ba, su riƙa wanke hannaye yadda ya kamata, su ƙarfafa tsaftar muhalli, su guje wa ta’ammali da dabbobin daji, su guji cin naman da bai dahu ba, su kuma tabbatar yana da tsafta, su kuma kawo waɗanda suka kamu da cutar zuwa asibiti a kan lokaci don samun magani.

Ma’aikatar ta bada lambobin waya da za a iya tuntuɓa idan an samu rahoton samun wannan cuta: lambobin su ne:
08039704476, 08034988560, 08050595019, 08176673447.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan