Matata Ta Hana Ni Kwanciya Da Ita Tsawon Shekara Ɗaya- Wani Miji Ya Faɗa Wa Kotu

342

Wani ɗan kasuwa, Malami Abdullahi, ya faɗa wa wata Kotun Shari’ar Muslunci mai zama a Magajin Gari dake jihar Kaduna cewa matarsa, Fatima Abubakar ta hana shi yin jima’i da ita tsawon shekara ɗaya.

Mista Abdullahi, wanda ke zaune a Rigasa, jihar Kaduna, ya kuma faɗa wa kotun ranar Laraba cewa Misis Abubakar tana yin lalata.

“Har yanzu ina son ta, kuma ina roƙon kotu da ta sasanta mu, kuma ta hana ta neman saki.

“Takan amsa waya daga mazaje daban-daban. Na tura ta gida don ta koyo yadda ake zaman aure.

“Na kai ƙarar ta ga iyayenta ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba. Suka roƙe ni, sai na dawo da ita gidana”, in ji Mista Abdullahi.

Tun da farko, Misis Abubakar, ta roƙi kotun ta hanyar lauyanta, Adamu Garba cewa tana son Mista Abdullahi ya sake ta sakamakon duka da yake yi mata.

“Yakan doki wadda nake wakilta koyaushe. Sau huɗu yana aika wa da kayanta gidan iyayenta. A ƙarshe dai, ya kore ta gida, kuma ya sake ta, amma ya dawo da ita bayan wasu watanni.

“Muna roƙon kotu da ta kawo ƙarshen wannan aure gaba ɗaya, ba za ta iya ci gaba da zama da shi ba”, in ji Mista Garba.

Bayan da alƙalin kotun, Mai Shari’a Muhammad Adam-Shehu ya saurari mutanen biyu, ya shawarce su da su sasanta kansu.

Mista Adam-Shehu ya ɗaga ƙarar zuwa 6 ga Fabrairu, don ba mutanen biyu damar sasanta kansu a wajen kotu.

Alƙalin ya kuma bada umarnin cewa dole waliyyan ma’auratan su bayyana a gaban kotun ranar 6 ga Fabrairun.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan