A ranar Talata ne Magatakardar Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandire, JAMB, Farfesa Is-haq Oloyede ya ce jami’an Hukumar Tsaro ta Nigerian Security and Civil Defense Corps, NSCDC, za su kama tare da gurfanar da duk wani jami’i gaban kotu matuƙar an same shi yana siyar da fama-faman Jarrabawar Bai Ɗaya ta Shig Makarantun Gaba da Sakandire, UTME ga ɗalibai sama da farashin da gwamnati ta amince na N4,000.
Ya ce ana shawarar ɗalibai da suka siyi fom daga wuraren siyar da fom ɗin da suka haɗa da Cibiyoyin Ɗaukar Jarrabawa Ta Kwamfuta, (Cibiyoyin CBT) masu zaman kansu da bankuna sama da farashin da aka amince da shi da su kai rahoto ofishin NSCDC mafi kusa.
Mista Oloyede, wanda ya yi wannan tsokaci a wani taron musayar ra’ayi da masu ruwa da tsaki a Hedikwatar NSCDC dake Abuja, ya ce a cikin N4,000, N3,290 ne kuɗin fom, N500 kuɗin kundin bayanai, sai N210 cajin banki.
Magatakardar ya ce kawo yanzu, an samu wani banki ɗaya da Cibiyoyin CBT da dama da makarantu a jihohin Anambara, Delta, Bayelsa, Inugu, Ribas da Adamawa da suka ƙara kuɗi, kuma an ɗauki matakin horo a kansu.
A yayin wannan taron musayar ra’ayin, an yi holin wani da ake zargi yana siyar da fama-faman a farashi sama da N4,000 a Wari dake jihar Delta.
A jawabinsa, Kwamanda Janar na NSCDC, Abdullahi Gana Mubammadu, ya ce kwamandojin jihohi na NSCDC da aka samu suna cin amanar da aka ɗora musu, su zargi kansu.
“Ya ce: “‘Yan Najeriya sun amince da ku ,kar ki ci amana. Idan kuka yi ba daidai ba, zan kore ku”.