Siyasar Kano: Dalilan Hijirar Ƴan Kwankwasiyya Zuwa Gandujiyya

414

Hakika idan ana maganar siyasa a Najeriya akayi maganar jihar Kano to ko shakka babu anzo ƙarshe, domin hakan ba zai zama abin mamaki ba idan akace mutumin kano ya kware wajen iya siyasa, domin sanin kowa ne a jihar Kano aka haifi fitattun ƴan gwagwarmayar siyasa irin su Malam Aminu, Malam Lawan Dambazau, Abba Mai Ƙwaru, Abubakar Rimi da sauransu.

Zamani ya sanya yanzu siyasar jihar Kano ta dauki wani sabon salo, domin yanzu idan ana maganar siyasa a jihar Kano to amon siyasar Kwankwasiyya da Gandujiyya kawai ake yi a da’irar siyasar jihar.

Kwankwasiyya Amana

Dariƙar Kwankwasiyya mai taken AMANA wacce tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon Sanata Kano ta tsakiya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ke jagoranta, ta kasance aƙidar siyasa ce wacce mabiyanta su ka yi imani da yadda Kwankwaso ya tafiyar da gwamnati a Lokacin ludayinsa yana kan dawo.

Ɗariƙar ta Kwankwasiyya ta yi fice wajen tarin dubun-dubutar matasa da su ka yi imani da tafarkin na Kwankwasiyya. Haka kuma Madugun na su yana da matuƙar tasiri a siyasar jihar Kano, ta hanyar dumbin magoya bayansa, da kuma fada aji a tsakanin magoya bayansa.

Gandujiyya Halacci

A ɗaya ɓangaren kuma Tsagin Gandujiyya mai taken HALACCI wacce magoya bayan gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje su ka yi dandazo a cikinta, duk da cewa kaso mafi yawa daga cikinsu sun ɓalle ne daga tsohon gidansu na Kwankwasiyya.

Tasirin mulki da karfin iko ya sanya Gandujiyya ke ƙamshin turaren Ɗan Goma, wanda hakan ke sanyawa jiga-jigan ɗariƙar KWANKWASIYYA ke yin hijira irin ta siyasa zuwa cikin GANDUJIYYA.

Hijirar Siyasa Daga Kwankwasiyya Zuwa Gandujiyya: Ina Dalili?

Batun sauya sheka al’amari ne daya zama ruwan dare a tsakanin ‘yan siyasa a faɗin ƙasar nan. Sai dai masana kimiyyar siyasa na ganin hakan koma baya ne ga ci gaban demokaradiyyar kasar nan.

Tun bayan da ƙasar nan to koma tafarkin demokaradiyya fiye da shekaru 20, manya, matsakaita da ƙananan ‘yan siyasa ke sauya sheka daga wannan Jam’iyya zuwa waccan.

A jihar Kano an fara samun hijirar ƴan Kwankwasiyya zuwa GANDUJIYYA a cikin watan Disambar Shekarar 2018 inda na hannun daman tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wato Janar Dambazau mai ritaya ya bayyana ficewarsa daga kungiyar Kwankwasiyya zuwa Gandujiyya.

Ficewar janaral Dambazau ta zama tamkar zaizayar ƙasa irin ta siyasa, domin kuwa ba a ci nisan zango ba manyan aminan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso su ka fice daga jam’iyyar PDP KWANKWASIYYA inda suka koma APC GANDUJIYYA.

Aminan Kwankwaso irin su Farfesa Hafiz Abubakar da Aminu Dabo – tsohon shugaban hukumar kula ta tasoshin jiragen ruwan ƙasar nan, Injiniya Muaz Magaji, marigayi Sanata Isah Yahaya Zarewa da kuma Babangida Sule Garo.

Sai kuma kwatsam aka tashi da labarin yadda shugaban rikon jamiyyar PDP KWANKWASIYYA Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi ya yi adabo daga ɗariƙar ta Kwankwasiyya tare da kamo taragon APC GANDUJIYYA.

Dalilin Da Ya Ke Haifar Da Wannan Hijirar

Hakika siyasar Kwankwasiyya tanada abin mamaki kwarai da gaske a jihar Kano . Domin siyasarsu ta nuna cewa MADUGUN DARIKAR KWANKWASIYYA mutum ne mai juriya da karfin hali sosai.

Dariƙa ce da take da goyon bayan matasa da yawa daga cikin al’ummar jihar Kano.

A ɗaya ɓangaren kuma an daɗe ana zargin Madugun na Kwankwasiyya da mulkin mallaka, rashin girmama abokan siyasa, zare idanu da kuma rashin karɓar shawara daga makusantansa.

Ga duk mai bibiyar kafafen yaɗa labarai ya san kalmar waɗanda su ka fice daga Ɗariƙar ta Kwankwasiyya ita ce rashin girmamasu tare da yi musu ƙarfa-ƙarfa.

Kamar yadda mu ka sani halayyar ɗan adam ce son inda za a mutunta shi a girmama shi tare da sauraron abin da zai faɗa, domin hakan yana cikin kyautatawa, ita kuma zuciya tana son wanda zai kyautata mata.

Yanzu dai dabara ta ragewa mai shiga rijiya, domin masu sharhi akan siyasa suna ganin muddin Madugun Kwankwasiyya bai sauya salon siyasarsa na girmama mutane tare da mutuntasu to hakika sai ya wayi gari sai shi kaɗai a cikin KWANKWASIYYA!

Muhammad Buhari Abba, dan jarida ne kuma ya rubuto daga Kano

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan