Tsakaninmu Da Kwankwaso Amana Ce: Duk Wuya Duk Runtsi Muna Nan Tare – Shehun Garu

635

Jagoran magoya bayan Kwankwasiyya na jihar Jigawa, Shehu M. Bello (Shehun Garu) ya bayyana cewa tsakaninsu da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso amana ce zalla. Don haka duk wuya duk runtsi suna nan tare da tsohon gwamnan Kano.

Shehun Garu ya bayyana hakan ne biyo bayan yadda rahotanmi ke yawo cewa wasu magoya bayan tsohon Sanatan na Kano ta Tsakiya suke ficewa daga tafiyarsa bayan hukuncin da kotun koli ta yanke kan zaben gwamnan Kano.

“To mu soyayyar Kwankwaso ba mu fara don mu daina ba. Don haka yanzu muka fara sonsa. Kuma muna tare da shi a koda yaushe.

“Amana daya ce, kuma za mu ci gaba da neman nasara a wurin Allah. Amana a zuci yake ba a baki ba. Makiyanka na kin ka Allah na sonka Madugu. Kai ne Dodon su”, cewar Shehu M. Bello.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan