Fiye Da Mata Miliyan Ɗaya Ne Su Ke Zubar Da Ciki Duk Shekara A Ƙasar Nan – Bincike

195

Sakamakon bincike da wasu likitoci suka yi ya nuna cewa akalla kashi 80 bisa 100 na mata ba su yin da dana sanin zubar da ciki.

Gidan talabijin din CNN ce ta wallafa sakamakon binciken wanda likitoci daga kasar Amurka suka yi.

Likitocin sun dauki tsawon shekaru Biyar suna yin wannan bincike akan mata gudq 1000 a kasar.

Bisa ga sakamakon binciken da suka yi likitocin sun bayyana cewa kashi 50 bisa 100 na matan da suka zubar da cikin sun shiga cikin rudadin tunanin ko su zubar da cikin ko a’a sannan kuma akalla kashi 70 bisa 100 daga cikin su sun ce sukan boye haka don kada mutane su rika nuna musu wariya.

Likitocin sun gudanar da wannan bincike ne domin gano ko da gaske ne zubar da ciki na iya haukatar da mace.

A dalilin haka ne mafi yawan kasashen Turai suka kafa dokar hana zubar da ciki.

Binciken dai ya tabbatar cewa mace za ta iya rasa ran ta idan ta zubar da ciki a wajen wanda bai da kwarewa amma ko kadan zubar da ciki baya haukatar da mace.

ABINDA BINCIKE YA BAYYANA

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa kashi 25 bisa 100 na mata na zubar da a duk shekara.

Sannan cire ciki musamman a wajen wadanda basu da kwarewa ya fi yawa ne a kasashen dake tasowa a duniya.

A Najeriya duk da cewa gwamnati ta kafa dokar hana zubar da ciki amma duk da haka akalla mata miliyan 1.25 ne ke zubar da ciki a duk shekara.

Wani binciken ma ya nuna cewa mata da dama a Najeriya na shan maganin da zai zubar musu da cikin da basu shirya wa ba ba sai sun je wani wuri ba.

Binciken ya kuma nuna cewa mutanen da basu da kwarewa kuma suke cire wa mata ciki sun fi yawa a kasar.

Sakamakon binciken da hukumar gudanar da bincike kan kiwon lafiya a Najeriya (NIMR) ta nuna cewa akalla mata 34,000 ke rasa rayukan su a dalilin rashin samun kwararrun likitoci a lokacin da duke bukatar zubar da ciki.

Premium Times

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan