Na Koma APC Ne Don Bada Gudunmawa Wajen Ci Gaban Kano- Bichi

879

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano, Rabiu Sulaiman Bichi, ya bayyana dalilansa na ficewa daga jam’iyyar zuwa jam’iyya mai mulki ta APC a jihar.

A ranar Talata Labarai24 ta kawo rahoton yadda Mista Bichi ya fice daga jam’iyyar PDP mai adawa tare da komawa jam’iyyar APC mai mulki.

Sai dai Mista Bichi ya bayyana ficewar tasa ne ranar Laraba da yammaci, kamar yadda BBC Hausa ta bada rahoto.

A wata hira da ya yi da BBC Hausa, ya ce ya koma APC ne saboda shugabannin jam’iyyar ne suka nemi ya koma domin bayar da gudummawarsa don ciyar da jihar Kano gaba.

Komawar tsohon shugaban na PDP dai ta zo ne kwana biyu bayan da Kotun Ƙolin Najeriya ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan Kano ranar Litinin, inda ta kori ƙarar da Abba Kabir-Yusuf, ɗan takarar gwamna na PDPn a Kano ya ɗaukaka gabanta, tare da tabbatar da Abdullahi Umar Ganduje a matsayin halattaccen gwamnan Kano.

A cewar BBC Hausa, wasu na ganin wannan ne dalilin da yasa Mista Bichi ya bar PDPn da kuma neman muƙami a APC.

Amma ya musanta hakan a hirarsa da BBC.

”Ita siyasa ta gaji haka, mutum in yana ganin zai ci gaba a wurin da yake to yana da ‘yancin yin hakan, in kuma yana ganin zai canza nan ma yana da ‘yanci, ai da muna cikin gwamnati muka ajiye”, ya shaida wa BBC Hausa haka.

Sai dai Mista Bichi bai ce uffan ba lokacin da BBC ta tambaye shi ko ya yi shawara da tsohon mai gidansa jagoran Kwankwasiyya na PDP, Rabi’u Musa Kwankwaso kafin yanke hukuncin ficewa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan