Rashin Nasarar Man United Yafi Nasararsu Yawa

265

Ayanzu haka wasu alkaluma sun nuna cewa rashin nasarar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United yafi nasararsu yawa tun bayan da aka tamkawa Ole Gunner Solskjaer kungiyar.

Wannan kididdiga ta biyo bayan rashin nasara da Manchester United din tayi ahannun kungiyar kwallon kafa ta Burnley awasan mako na 24 ajiya.

Manchester United dai abubuwa naci gaba da tabarbaremusu akarkashin mai horas war na yanzu.

Ayanzu haka kungiyoyin kwallon kafa guda 6 na karahen teburin gasar ajin Premier ta kasar Ingila akakar wasa ta bana dukkaninsu babu wadda bata lashe Manchester United ba, kungiyoyin kwallon kafan dasuka hadar da Burnley da Watford da Bournemouth da Newcastle da West Ham United da kuma Crystal Palace.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan