Dole Myanmar Ta Kawo Ƙarshen Kisan Kiyashi Da Ake Yi Wa Musulmin Rohingya- ICJ

221

Dole Myanmar ta ɗauki matakan gaggawa domin kawo ƙarshen abinda aka siffanta a matsayin kamfe na kisan kiyashi da ake yi wa Musulmin Rohingya, Kotun Shari’a ta Ƙasa da Ƙasa ta yanke hukuncin haka a wata nasara ta farko da masu sukar ƙasar suka yi, a cewar Independent, jaridar Birtaniya.

Mai Shari’a Abdulqawi Ahmed Yusuf ya ce kotun ta samu Rohingya “a haɗarin zama wajen kisan kiyashi”.

Independent ta ce gungun alƙalai 17 sun goyi bayan ƙaƙaba wa Myanmar matakai don ta tabbatar da cewa dakarun sojinta ba su aikata laifukan kisan kiyashi ba, sannan ta ɗauki matakai don hana kashe-kashe da cutar da Rohingya.

An umarci Myanmar da ta ƙiyayya duk wata hujja da kotun za ta iya amfani da ita a zamanta na gaba, kuma ta kai wa kotun rahoton duk matakan da aka umarce ta ta ɗauka cikin wata huɗu, sannan ta riƙa kai rahoto duk bayan wata shida, yayinda ƙarar ke shirin zuwa gaban Babbar Kotun Majalisar Ɗinkin Duniya.

Kotun ta ƙara da cewa umarninta na tilas ne, kuma “ya tanadi dokokin ƙasa da ƙasa” kan Myanmar.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama sun yi maraba da wannan mataki.

“Umarnin ICJ kan Myanmar na ta ɗauki ƙwararan matakai don kawo ƙarshen kisan kiyashin da ake yi wa Rohingya wani babban mataki ne da zai kawo ci gaba da zalunci da ake yi wa ɗaya daga cikin al’umomin da aka fi zalunta a duniya”, in ji Param-Preet Singh, Daraktan Ƙasa da Ƙasa na Human Rights Watch dake New York.

“Ya kamata gwamnatoci da hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya su shigo ciki a halin yanzu don su tabbatar da cewa an yi amfani da wannan umarni yayinda ake shirin gabatar da ƙarar kisan kiyashin zuwa gaba”, in ji shi.

Daraktan Yanki na Amnesty International na Asia ta Kudu, Nicholas Bequelin, ya ce: “Hukuncin yau yana tura saƙo ga manyan jami’an gwamnatin Myanmar: duniya ba za ta lamunci zalunce-zaluncensu ba, kuma ba za ta karɓi hujjojinsu marasa ƙwari ba bisa abinda ke faruwa a zahiri a Jihar Rakhine a yau.

“Kimanin mutane 600,000 na Rohingya waɗanda suke can har yanzu ana hana su haƙƙoƙinsu lokaci-lokaci kuma cikin dabara. Suna fuskantar tsantsar zalunci a nan gaba.

“Dole Myanmar ta yi biyayya ga umarnin ICJ kuma ta ɗauki matakin gaggawa don kawo ƙarshen karya doka da ake yi wa waɗannan al’umomi, kuma ta hana lalata hujjoji”, a kalaman Mista Bequelin.

Aung San Suu Kyi, Shugabar Myanmar, ta amince cewa an aikata laifukan yaƙi, amma ta musanta cewa akwai kisan kiyashi a wata muƙalla da aka wallafa sa’o’i kafin hukuncin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan