Mujiya Ta Kai Wa Gwamnan Jihar Benue Hari A Lokacin Da Ya Ke Addu’a A Coci

93

Jim kaɗan da tabbatar da nasarar gwamnan jihar Benue Samuel Ortom da kotun ƙolin ƙasar nan ta yi, gwaman ya shiga wata coci a birnin Makurdi domin addu’a tare da godiya ga Ubangiji.

Bayan da gwamnan ya shiga cocin ne sai wani abin firgici da mamaki ya faru, inda wata mujiya da ake zaton ta sihiri ce ta shigo cocin a dai-dai lokacin da Ortom ya gurfana domin yin addu’o’in godiya ga ubangiji.

Cikin wani rahoto da jaridar Daily Post ta ruwaito, Ortom ya je cocin ne domin godiya ta musamman ga ubangiji a kan nasarar da ya samu amma sai ga mujiya ta shigo.

Wani da abin ya faru akan idonsa mai suna Prince Tordue Abe, ya bada labarin yadda mujiyar ta bayyana a cocin a dai-dai lokacin da Gwamnan ke godiya a kan nasarar sa kuma ta nufi gwamnan ba kakkautawa.

Amma wasu matasa da ke cocin sun hanzarta kama mujiyar wacce ta so sauka a tsakar kan gwamnan. Mutane da yawa da ke wajen sun dinga mamakin yadda aka yi mujiyar ta shigo cocin da yadda ta tunkari gwamnan a tsakiyar kan shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan