Ku Sa ‘Ya’yanku Makaranta Ko Ku Baƙunci Gidan Yari, El-Rufa’i Ya Gargaɗi Iyaye

260

A ranar Juma’a ne gwamnatin jihar Kaduna ta shawarci iyaye su tura ‘ya’yansu makaranta ko su fuskanci gurfana a kotu kamar yadda dokoki suka tanada.

Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Ilimi, Phoebe Yayi ta bada wannan shawara a Kaduna a yayin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN.

Mista Yayi ta jaddada cewa duk wani yaro yana da haƙƙi a ba shi ilimin firamare da na sakandire kyauta kuma wajibi, tana mai ƙarawa da cewa nauyi ne a kan gwamnatin jihar Kaduna ta bada wannan ilimi.

Ta ce a wajen cimma wannan buƙata, gwamnati ta mayar da ilimi kyauta ga kowane yaro tun daga firamare har zuwa sakandire a jihar.

Mista Yayi ta bayyana cewa wannan shiri yana daga cikin matakan da aka ɗauka don tabbatar da cewa duk wani mazaunin jihar ya iya rubutu da karatu don samun kyakkyawar rayuwa.

“Saboda haka, iyaye ba su da wani uzuri da zai sa su ƙi kai ‘ya’yansu makaranta saboda gwamnati ta ɗauke dukkan hidindimun kuɗi daga iyaye.

“Ya kamata ku san cewa Dokar Kare Yara da Walwalarsu ta 2018, Sashi na 18 (6) ta tanadi cewa duk wani mahaifi/ mahaifiya ko wakili da ya ƙi/ ta ƙi kai ɗansa/ ‘yarta makaranta ya/ ta aikata laifi.

“Dokar ta ƙara da cewa idan aka kama mahaifi/ mahaifiya ya/ ta saɓa wa dokar a karon farko, za a yanke masa/ mata hukuncin aikin gayya, idan kuma ya/ ta ƙara saɓa wa dokar a karo na biyu, za a ci tarar sa/ ta, ko ya/ta yi zaman gidan yari, ko duka biyun.

“Saboda haka, tura ‘ya’yanku makaranta ba zaɓi ba ne, wajibi ne, kuma gaza yin haka babban laifi ne da zai iya jawo zaman gidan yari”, in ji ta.

Ta yi gargaɗin cewa ba wani dalili da zai sa mahaifi/ mahaifiya ya hana ɗansa/ ta hana ‘yarta haƙƙin samun ilimi, ilimin da zai buɗe wa yaron damar samun kyakkyawar rayuwa.

Babbar Sakatariyar ta ƙara da cewa har manyan mutane an ba su dama ta biyu su nemi ilimi don “kar a bar kowa a baya”.

Ta jaddada shirin gwamnati na zuba kuɗaɗen da suka wajaba a ilimi, kyautata wuraren koyo, ta kuma tabbatar da ingancin koyo da koyarwa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan