Hajia Hama Aware Ta Bayar Da Tallafi A Ƙananan Hukumomin Kura Da G/Malam

272

A ƙoƙarinta na magance matsalar talauci tare da samar sa sana’o’in dogaro ga al’ummar yankin Kura, Madobi da Garun Malam, mai baiwa gwamna Abdullahi Umar Ganduje, shawara akan harkokin zuba jari, Hajia Hama Ali Aware Garun Malam, ta rabawa al’ummar mazaɓun Rugar Duka da ke ƙaramar hukumar Kura da Garun Babba a yankin ƙaramar hukumar Garun Malam tallafin Kuɗi domin fara sana’a.

Hajia Hama Aware wacce ta samu wakilcin babban hadiminta na musamman Alhaji Sulaiman Garun Malam, ta baiwa mata da matasan waɗannan mazaɓu tallafin Kudi domin samun jarin da zai tallafi rayuwarsu.

Tun da farko Hajia Hama, ta bayyana cewa babban burinta shi ne ganin al’ummar yankin da fito sun amfana da romon demokaradiyya, tare kuma da ganin sun fita daga zafin radadin talauci.

“Babban burina shi ne ganin mata sun samun sana’ar da za su dogara da ita, haka kuma akwai buƙatar a taimaki matasa da jari, domin su ne manyan gobe”

Ta ƙara da cewa tallafin na ta ba wai ya tsaya ga waɗannan mazaɓu ba kawai, a’a za a cigaba da yi zuwa sauran mazaɓun da su ke ƙananan hukumomin Kura, Madobi da Garun Malam

Waɗanda su ka amfana da wannan tallafi sun bayyana matuƙar jin dadinsu, tare da yin addu’ar samun nasara ga Hajia Hama Aware a dukkanin al’amuranta.

A ƙarshe ta yi kira ga waɗanda su ka amfana da wannan tallafi da su yi amfani da shi ta hanyar da ta ce, ta kuma buƙaci al’ummar wannan yanki da su cigaba da baiwa gwamna Abdullahi Umar Ganduje goyon baya a ko da yaushe

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan