Hotunan Ziyarar Malaman Jami’ar Bayero A BBC Landan

271

Tawagar malaman tsangayar sadarwa ta jami’ar Bayero da ke Kano, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Umaru Pate da Dakta Nura Ibrahim sun kai ziyarar aiki gidan radiyon BBC Hausa da ke birnin Landan.

Sauran ƴan tawagar sun haɗa da Dakta Hadiza Jummai Ibrahim da kuma Daktar Maryam Mukhtar.

Ana sa ran dai wannan ziyara za ta haifar da kyakykyawar dangantaka tsakanin tsangayar sadarwa, jami’ar Bayero da kuma gidan radiyon BBC Hausa.

Tun da farko dai tsangayar sadarwar ta dade da mallakar gidan rediyo, wanda ya ke watsa shirye-shiryesa a ƙaramin zango, daga baya kuma hukumar kula da kafafen yada labarai ta ƙasa NBC ta baiwa jami’ar Bayero lasisin samar da gidan talabijin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan