Ina Matuƙar Godiya Ga Gwamna Ganduje Da Abdullahi Abbas – Jibrin Kofa

992

An yi zaben Kiru da Bebeji ranar Asabar 25 ga watan Janairun 2020 kamar yadda hukumar zabe ta tsara. Magoya bayana sun fito kwansu da kwarkwatarsu don sauke nauyin da ya rataya a wuyansu amma sai a ka yi amfani da karfin tuwo a dukkan mazabu a ka hana su ‘yancinsu na zabar wanda su ke so bisa tanadin doka. A garin Kofa ne kawai su ka samu tirjiya kuma su ka kasa shiga su yi ta’annatin da su ka shirya yi. Mun sani cewa mu muka ci zabe amma a ka murde mana da karfi da yaji.

Duk da cewa a akasarin mazabu ba’a yi zabe ba, amma abin mamaki sai aka karkata akalar akwatunan zabe kuma a ka kirkirin sakamakon boge. Za mu ajiye shaidar tarzomar da su ka tayar, da ta’addancin da aka yi da murdiyar da a ka yi don ’yan baya su gani.

Duk da cewa ina da ja akan sakamakon da hukumar zabe ta fitar, amma na fawwalawa Allah (SWT). ‘Yan sanda da sauran jami’an tsaro su shaida ne akan abin da ya gudana amma hukumar zabe ta yi burus ta bawa abokin hammayyata nasara duk da cewa bai samu halastassun kuri’uba kamar yadda doka ta tanadar. Ina da yakinin cewa duk wanda aka dorawa nauyin tabbatar da adalci amma ya ci amana, to kuwa hukuncin Ubangiji zai tabbata a gareshi.

A matsayina na Musulmi na dauki wannan kaddara da Allah ya kawo, kuma ina taya abokin hamayyata Ali Datti Yako murna. Ina fatan zai ci gaba daga inda na tsaya bayan shafe shekaru da dama ina hidimtawa al’umma. Kuma na sha alwashin ba shi shawarwari da gudunmawar da ta dace domin samawa jama’a wakilci nagari. Ina mai sanar da duniya cewa ba zan kai kara kotu ba.

Ina mai matukar mika godiya ga Shugaban Kasa da Mataimakin Shugaban Kasa da Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisa da Sakataren Gwamnatin Tarayya da Shugaban Jam’iyyarmu ta APC na kasa da Gwamnan Jihar Kano da Gwamnatin Jihar Kano da Shugaban Gwamnonin Nigeria da abokan aikina a Majalisa ta bakwai da Majalisa ta Takwas da Majalisa ta Tara.

Ina jaddada godiya ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Khadimul Islam da Shugabanin Jam’iyyarmu ta APC a matakin jiha da kanan hukumomi da mazabu.

A karshe ina mika godiyata ga al’ummar Kiru da Bebeji bisa goyon baya da kauna da su ka saba bani na wakilsu har karo uku. Na sha alwashin ci gaba da taimakawa don cigaban jama’a da jam’iyyarmu ta APC a matakin jiha da matakin kasa da matakin mazabu.

Na gode.

Abdulmumin Jibrin DanKofa PhD
(Jarman Bebeji)

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan