Tun daga ranar 21 ga watan Janairun shekarar 2020 miliyoyin ‘yan China suka fara shirin bikin sabuwar shekararsu ta gargajiya wadda kuma shekarar bana ta beraye ce.
Bisa al’ada dai duk shekara ‘yan China kan zabi dabba cikin dabbobi 12, su ne bera, takarkarin saniya (ox), damisa, zomo, dodo (dragon), maciji, doki, akuya, zakara, kare da kuma alade.
Saboda haka duk shekara 12 za a saka wa wata shekara sunan daya daga cikin wadannan dabbobin.
2018 Shekarar Kare ce, 2019 Shekarar Alade, 2020 kuma Shekarar Bera ce.
Sai dai, yayin da ‘yan China ke wannan biki, a Najeriya kuwa gudun beran ake yi sakamakon bullar zazzabin Lassa a baya-bayan nan mai saurin kisa, wadda beran ke yadawa.
Ana fara bikin Sabuwar Shekarar Gargajiya ta Lunar a China ranar 25 ga watan Janairu, ba kamar yadda aka saba ba wato 1 ga watan Janairu.
‘Yan China na mutunta bera
A China ana kallon bera a matsayin alamar arziki da wadata, kuma shi ne kan gaba a cikin dabbobin da suke girmamawa duk shekara.
Wata tatsuniyar kasar ta ruwaito cewa wani sarki ne a kasar ya ce duk dabbar da ta riga zuwa wurin shagalin biki ita za a zaba.
Saboda haka sai bera ya ce da takarkarin saniya (ox) ta taimaka ta rage masa hanya.
Ana zuwa wurin shagali sai bera ya yi tsalle ya fado daga bayan saniya kuma ya shiga gaba.
A al’adance ma’aurata a China kan yi addu’a ga bera tare da fatan su samu haihuwa kamar yadda bera ke haihuwa.
Sun yi imanin cewa mutanen da aka haifa a Shekarar Bera sun fi kuzari da kwarin gwiwa.
BBC Hausa
