Kasar Saudiyya Za Ta Dakatar Da Bayar Da Tallafi Ga Masallatan Duniya

169

Tsohon ministan shari’a na kasar Saudiyya, Mohammed Bin Abdul-Karim Issa, ya bayyana cewa kasar sa za ta dakata da bayar da tallafi ga Masallatan kasashen duniya, Arabi21.com ta ruwaito hakan a ranar Juma’ar nan da ta gabata.

Cikin wani rahoto daa Jarida kasar Switzerland mai suna Le Matin Dimanche, ta bayyana cewa kasar Saudiyya za ta kirkiri kananan hukumomi na gudanarwa ga kowanne Masallaci, tare da hadin guiwar hukumomin yankin, domin mika wannan Masallatai a hannun amintattu.

Ministan ya kara da cewa: “Lokaci yayi da zamu mika Masallacin Geneva ga majalisar gudanarwar kasar Switzerland wacce ke wakiltar Musulmai a yankin. Sannan za a zabi babban Malami.”

Ya ce Saudiyya za ta dauki irin wannan mataki akan kowanne Masallaci na duniya, inda ya ce kasar za ta yi haka ne saboda wasu dalilai na tsaro.

Ministan dai ya jagoranci wata tawaga a ranar Alhamis dinnan zuwa sansanin Auschwitz, domin halartar bikin cika shekaru 75 da samun ‘yancin.

Ya nuna rashin jin dadinsa akan Yahudawa da aka kashe sakamakon kisan kiyashin da aka yi a lokacin yakin duniya na biyu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan