Annabi Muhammad (SAW), Ma’aunin Zaman Lafiya Da Jin Ƙai – Rochas Okrocha

773

Tsohon gwanan jihar Imo kuma Sanata mai wakiltar Imo ta yamma, Rochas Okrocha, ya bayyana Annabi Muhammad SAW a matsayin bangon ma’aunin zaman lafiya da hadin kai.

Rochas yayi kira ga al’ummar Musulmi da su rika yin koyi da Shugaba SAW wajen tafiyar da rayuwarsu domin tabbatar da zaman lafiya da jin kai.

“Akwai muhimman darussan da za’a koya daga rayuwa da koyarwar Annabi Muhammadu SAW. Ya kasance ginshikin aminci da haɗin kai.”

Rochas Okrocha ya bayyana haka ne ta hannun mataimakinshi a fannin labarai, Ahmad Mustapha, a ranar Litinin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasa, NAN, ya rawaito.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan