Ganduje Zai Ciyo Bashin Biliyan N15 Don Aiwatar Da Shirin Ilimi Kyauta

331

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nemi sahalewar Majalisar Dokokin Jihar Kano don ta ba shi dama ya karɓo bashin biliyan N15 daga Guaranty Trust Bank (GT Bank) don aiwatar da shirinsa na ilimi kyauta.

A ranar Litinin ne Kakakin Majalisar Dokokin ta Jihar Kano, Abdul’azeez Garba-Gafasa ya karanta wasiƙar da Gwamna Ganduje ya aiko, inda yake neman amincewar su.

A cewar Mista Garba-Gafasa, ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano za su ci moriyar bashin idan aka sahale.

A cewar wasiƙar, ana son ciyo bashin ne don ba ƙananan hukumomin damar tabbatar da nasarar shirin gwamnatin jihar na ilimi kyauta kuma wajibi.

Kakakin Majalisar ya ƙara da cewa idan aka amince a ciyo bashin, kowace ƙaramar hukuma daga cikin ƙananan hukumomin 44 na jihar Kano za ta samu miliyan N340 don tabbatar da ɗorewar shirin na ilimi kyauta kuma wajibi.

Wasiƙar, a cewar Kakakin, ta ce za a biya bashin ne a cikin watanni 30, da kuɗin ruwa da ya kai kaso 15%.

Mista Garba-Gafasa ya ce za a riƙa cire bashin ne daga kason ƙananan hukumomi na wata-wata da gwamnatin tarayya ke ba su.

A cewar majiyarmu, jim kaɗan bayan karanta wasiƙar, sai Kakakin Majalisar ya miƙa ta zuwa ga Kwamitin Majalisar na Ƙananan Hukumomi don duba buƙatar ciyo bashin.

Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Kabiru Hassan-Dashi shi zai sa ido a aikin kwamitin.

Gaba ɗaya ‘yan Majalisar Dokokin sun amince kwamitin ya gabatar da rahotonsa cikin kwanaki biyu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan