Gwamnatin jihar Legas, ta haramta baburan haya da aka fi sani da Okada da kuma Keke Napep, babura masu kafa uku, a wasu kananan hukumomi, gadoji da kuma manyan hanyoyin dake jihar.

Sanarwar da mai baiwa Gwamna Babajide Sanwo-Olu shawara kan kafofin yada labarai Jubril Gawat ya fitar, ta ce haramcin hayar ya shafi baburan kamfanonin sufuri na Opay da kuma Gokada.

Sanarwar ta kuma ce dokar haramta hayar baburan za ta soma aiki daga ranar 1 ga watan Fabarairun dake tafe.
Daga cikin kananan hukumomin jihar ta Legas 15, da kuma manyan yankunan da dokar ta shafa, akwai, Apapa, Apapa Iganmu, Lagos Mainland, Yaba, Surulere, Itire Ikate, da Coker, da kuma Aguda.
Sauran yankunan sun hada da Lagos Island, Ikeja,
Eti-Osa, Ikoyi da Obalende, Lagos Island ta gabas, sai kuma Ojodu, Onigbongo da kuma Iru Ikoyi zuwa Obalende.
[…] Muƙalar Da Ta GabataGwamnatin Jihar Legas Ta Haramta Sana’ar Achaɓa Da Keken Napep […]