Shekaru 3 Da Mutuwar Bello Masaba Mijin Mata Sama Da 100

212

Baba Masaba, wanda asali mutumin garin Bidda ne da ke jihar Niger, ya mutu ranar asabar, 28 ga watan Janairun shekarar 2017.


Rahotanni sun ce ya mutu ne yana da shekara 93, inda ya bar ‘ya’ya kimanin 137.


Baba Masaba dai ya yi fice ne saboda yawan mata da ‘ya’yansa.


Shi dai marigayin – wanda ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya – ya fito fili ne bayan da a wata hira ta musamman da ya yi da sashen Hausa na gidan rediyon BBC, ya ce ya auri mata 86 kuma dukkansu suna tare da shi a lokacin, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce tsakaninsa da Malaman addinin Musulunci.


Bayanai sun nuna cewa Baba Masaba yana biya wa duk iyalinsa bukatunsu na rayuwa duk kuwa da yawansu.


A wani lokaci can baya ma jami’an tsaro sun taba tsare shi a birnin Minna na jihar, saboda auren mata rututu, abin da ya saba wa addinsa na Musulunci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan