Yadda Kotu Ta Samu Maryam Sanda Da Laifi

247

A ranar Litinin ne Babbar Kotun Birnin Tarayya, Abuja ta samu Maryam Sanda da laifin kashe mijinta, Biliyaminu Bello.

Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Yusuf Halilu ya yanke wa Misis Sanda hukuncin kisa ne ta hanyar rataya.

Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya ta tuhumi Misis Sanda nda laifin kisan kai a watan Nuwamba, 2017, ta kuma roƙi kotun da ta yanke wa wadda ake zargin hukuncin kisa.

Wanda aka kashe ɗin, Mista Bello, ɗa ne ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Halliru Bello.

Mai Shari’a Halilu ya ce an samu gamsasshiyar hujja da ta tabbatar da cewa wadda ake zargin ta aikata kisan.

Alƙalin ya yi watsi da iƙirarin Misis Sanda cewa mijinta ya faɗa kan fasasshiyar tukunyar Shisha ne a lokacin da suka yi faɗa a ranar da wannan mummunan al’amari ya afku.

Ya ce hujjar da ake da ita ta nuna cewa wadda ake zargin ta caka wa mijinta wuƙa wuƙa da nufin “kisa”.

A lokacin da alƙalin ya sanar da cewa an samu Misis Sanda da laifi, wadda ake zargin ta yi yunƙurin guduwa daga kotun, yayinda ‘yan uwanta suka fara ihu da kururuwa, a wani yunƙuri na neman tausayawa daga jama’a.

Alƙalin ya banda hutu da nufin dawowa da nutsuwa a kotun kafin ya yanke hukuncin.

Tunda farko, majiyarmu ta PREMIU TIMES ta bada rahoton yadda aka janye tuhumar da ake yi wa Maimuna Aliyu, mahaifiyar Misis Sanda, Aliyu Sanda, ɗan uwanta da Sadiya Aminu, ‘yar aikinta bisa zargin su da neman rufe hujja ta hanyar goge jinin da sauran hujjoji daga wajen da aka aikata laifin.

An yi kusan shekara uku ana sauraron ƙarar sakamakon jinkiri, yawan ɗage-ɗage da kuma gazawar shaidu na bayyana a gaban kotun.

Bayanin Shaidu
Taɓarɓarewar aure tsakanin Maryam da marigayi Biliyaminu ta kai matuƙa ne a daren 18 ga watan Nuwamba, 2017. Shaidu da dama da suka haɗa da na wadda ake zargi ta ce wannan mummunan al’amari ya afku ne sakamakon zazzafar sa-in-sa tsakanin ma’auratan a wannan dare da wannan mummunan al’amari ya afku.

An zargi Misis Sanda da yi wa mijinta barazana sau da dama, har da barazanar yanke masa azzakari idan ya ƙi sakin ta, in ji Ibrahim Mohammed, ɗaya daga cikin shaidu shida da mai shigar da ƙara ya gabatar, kamar yadda rahoton PREMIUM TIMES ya nuna.

Wannan shaida ya faɗa wa kotun cewa ya kasance tare da mamacin a wannan dare fiye da sa’o’i takwas.

Mista Mohammed, abokin Biliyaminu, ya ce sa-in-sar tasu ta koma faɗa.

Mista Mohammed ya ce ya yi ƙoƙarin cire hannun Misis Sanda daga wuyan mijinta kafin cikin gaggawa ta fasa kwalbar man gyaɗa a jikin bango ta kuma yi ƙoƙarin caka wa mijinta ita.

“Na riƙe hannayenta Biliyamin kuma ya je bayanta ya ƙwace kwalbar daga hannunta.

“Ta ce ba za ta daina ba sai Biliyamin ya sake ta a wannan dare; ta ce ko dai ya sake ta ko ta yanke masa azzakari”, in ji shaidar.

Mista Mohammed ya ce a gabansa Misis Sanda ta ci gaba da barazanarta yayinda ta ci gaba da kai wa marigayin hare-hare.

Shaidar ya bada labarin cewa wadda ake zargin ta farko ta yi wani yunƙurin na kashe mijinta bayan ta fasa wata kwalbar turare, amma mijin nata ya ƙwace kwalbar.

“Daga nan sai wadda ake zargin ta farko ta ɗauko wata wuƙa wadda ta so ta caka wa mijin nata”, ya ƙara da haka.

Wannan shaida ya ce marigayin, abokinsa ya samu raunuka da yawa yayinda yake ƙoƙarin ƙwace kwalbar daga matar tasa.

Mista Mohammed ya ce ya bar gidan tare da wani abokinsa wanda ya kira don ya raba faɗan, yana tunanin cewa komai ya dawo daidai, kawai sai dai ya ji labarin mutuwar abokinsa da safe.

“Na je Asibitin Maitama da safe na samu Biliyaminu kwance a kan gado a gaban asibitin. Akwai rami a ƙirjinsa kusa da zuciyarsa, akwai cizo a cikinsa. Akwai yanka a cinyarsa kuma akwai alamar ɗinki a jikinsa.
Bayanan Sanda
A shaidar da ta bayar a gaban kotun, Misis Sanda ta amince cewa auren wanda ya yi shekara biyu, kuma aka haifi ‘ya mace ya gamu da cikas.

Amma ta musanta kashe mijinta ko kuma niyyar yin haka. Misis Sanda, mai ‘ya ɗaya ta ce matsala ta fara afkuwa ne bayan ta ga hotunan wata mata tsirara a wayar mijin nata, shi ne ta tunkare shi.

Misis Sanda ta ce ta buƙaci ya sake ta kafin a fara hayaniya, hayaniyar da ta kai su tsakar dare, ta kuma zama faɗa.

“Ya ture ni, na faɗi ƙasa, ban sani ba na fasa kwalbarsa ta Shisha, ruwan da yake ciki ya malale a tsakar ɗaki. Ya ture ni ƙasa, sai na ji ‘yarmu tana kuka. Na faɗa masa ya ƙyale ni in lallashe ta”, in ji ta.

Wadda ake zargin ta ce mamacin ya faɗo kan fasasshiyar tukunyar Shishar ne a ƙoƙarin ƙara riƙe ta. “Sai na ga fasasshiyar kwalba ta shiga ƙirjinsa wadda na cire, na rufe wajen da siket”.

Matashiyar ta ce daga nan ne sai ta yi maza ta kai shi Babban Asibitin Maitama inda aka tabbatar ya rasu.

Ana zargin dangin Misis Sanda da goge wajen da aka aikata laifin, kuma ba a gudanar da binciken gano musabbabin mutuwar Mista Bello ba.

Regina Okotie-Eboh, lauyar wadda ake zargi ya ce masu shigar da ƙara sun gaza kawo hujjar zarge-zargensu. Ta ce mai ƙarar ba ta kira malaman jiyya ko likitoci ba daga inda aka kai mamacin a matsayin shaida.

Misis Okotie-Ebor ta ƙara da cewa sun gaza kawo wuƙar da wadda ake zargi ta yi amfani da ita wajen aikata kisan.

A watan Disamban bara ne alƙalin ya tsayar da 27 ga Janairu, 2020 don yanke hukunci.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan