Masana kiwon lafiya sun binciko cewa yawan cin jan nama, ma’ana naman babbar dabba yana kara wari a jikin ɗan adam.
Ana samun Warin jiki ne dai sakamakon yadda ƙwayar bakteriya ke dagargaza sinadarin furotin mai nau’in ruwa, wanda ya ke dauke da sinadarin haidorijin, wanda hakan ke da tasiri wajen ƙaruwar warin jiki
Tun da farko dai an wallafa sakamakon Bincike a Mujallar Chemical Senses ta shekarar 2006.
Sakamakon Binciken ya kara da cewa; warin jiki yana ƙara samun sararin zama idan ya samu mutum mai cin jan nama sosai.
A ƙarshe sakamakon binciken yace ba iya cin naman bane yake kawo wa jiki wari ba, amma dai abinda yake da akwai shi ne, jikin masu cin Jan Nama yafi wari.


Turawa Abokai
[…] Muƙalar Da Ta GabataYawan Cin Nama Yana Kawo Warin Jiki – Binciken Masana […]
Sharhi:allah.yaba wannan jarida damar kawo muna labarai masu dadi