Za A Shuka Zogalen Naira Bilyan 9 A Faɗin Ƙasar Nan

232

Kungiyar Masu Masana’antu ta Najeriya (MAN), ta bayyana cewa ta kammala shirye-shiryen fara gagarimin aikin dashen zogale a kadadar gonaki daban-daban a kananan hukumomi 774 na Najeriya.

Shugaban Kuniyar MAN, Micheal Ashimashiga ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya kira a karshen makon da ya gabata, a Abuja.

Da ya ke bayyana muhimmancin zogale da kuma yawan aikin, Ashimashiga ya ce aikin zai ci kudi kamar naira bilyan 9.

Wannan shiri a cewa shugaban kungiyar masu masana’antun, ya na daya daga cikin shirin da ake kirkirowa domin samar da aikin yi kasar nan.

Ya ce wannan kungiyar ta su na da mambobi 5,000, kuma daga zuwa faduwar ruwan damina za a shuka zogale milyan 10 a fadin kasar nan, a matsayin somin-tabin farawa.

Ya ce za a rika monawa ko dasawa ana sayarwa saboda tsananin bukatar zagalen da ake yi a kasar nan da ma kashen waje da dama.

“Saboda dai mun lura cewa ci gaban kasar nan ya dogara ne kacokan a kan harkokin noma. Shi kuma ganyen zogale ya na da muhimmanci ga kiwon lafiya da kuma inganta tattalin arziki.” Inji Ashimashiga.

Ya ce duk manomin da ya shuka zogale, to ita kungiyar ce za ta rika saye zogalen daga hannun su kai-tsaye.

Sai kuma ya kara cewa MAN ta kulla yarjejeniyar wannan tsarin cinikayya ne da abokan hulda na kasashen waje, domin samar wa matasa dimbin ayyukan yi.

Sannan kuma ya ce za a raba wa mai noman zogale irin da zai shuka da kuma filin da zai yi noman duk kyauta.

Ashimashiga ya ce duk da Najeriya ce kasar da ta fi samar da zogale mai kyau, sai ga shi kasashen Indiya da Chana ne ke cin moriyar noman zogale a duniya, saboda na Najeriya babu shi a kasuwannin duniya.

Noman zogale na da muhimmanci. Saboda zogalen da manomi zai noma a cikin hekta 1, to shinkafar da aka noma cikin hekta 50 ba za ta kai yawan sa ba.” Cewar Ashimashiga.

Premium Times

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan