An Yi Min Wahayi Ba Za A Rataye Maryam Sanda Ba – Fasto

254

Fasto Apostle Chris Omashola ya bayyana wahayin da aka yi masa akan Maryam Sanda, matar da aka yankewa hukuncin kisa a farkon makon nan a babbar kotun Abuja.

Maryam dai an kama ta da laifin kashe mijinta, Bilyaminu, wanda yake da ne a wajen tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Halliru Bello.

‘Yan sanda suna zargin Maryam da kashe mijin da kwalba da misalin karfe 3:50 na daren ranar 18 ga watan Nuwambar shekarar 2017.

Sai dai kuma Fasto Apostle Omashola wanda a kwanakin baya ya bayar da wahayin da aka yi masa akan fitaccen mawakin nan na jihar Legas, Naira Marley, ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Twitter, inda ya ce ya gano cewa baza a rataye Maryam Sanda ba.

A cewar sa Allah ya nuna masa hakan cewar baza a rataye Maryam Sanda ba.

Omashola yayi rubutu kamar haka: “Ban san komai game da Maryam Sanda ba, kawai dai na san halin da ake ciki game da shari’arta jiya, ta gode Allah na gano cewa za ta rayu.

“Allah ya ce Maryama Sanda ba za ta mutu ta hanyar rataya ba, ban san yadda hakan zai kasance ba, amma dai wannan shine abin Allah ya nuna mini a lokacin da nake addu’a. Ku taya ta da addu’a.”

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan