Gwamna Ganduje Ya Halacci Bikin Rantsar Da Ƴan Majalissun Da Su Ka Lashe Zaɓe

190

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya halarci bikin rantsar da sababbin yanmajalisar wakilai guda 3 na jihar Kano da aka sake zabar su a satin da ya wuce

Ƴan majalisar waɗanda suka haɗa da Honarabul Alhassan Ado Doguwa da Honarabul Munnir Babba Dan’agundi da kuma Honarabul Ali Datti Yako.

An yi bikin rantsuwar ne a zauren majalisar tarayya wadda Kakakin ta Honarabul Femi Gbajabiamila ya jagoranta.

Gwamna Ganduje ya samu rakiyar Sanata Ibrahim Shekarau da Sanata Kabiru Gaya da kuma Sanata Barau Jibrin, sai kuma shugaban Jam’iyar APC na jiha Alhaji Abdullahi Abbas

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan