Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da buƙatar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar mata, inda yake roƙon ta amince ya ciyo bashin biliyan N15 daga bankin Guaranty Trust Bank (GTBank) don aiwatar da shirin gwamnatisa na ilimi kyauta kuma wajibi.
Majiyarmu ta bada rahoton cewa a yau Laraba ne Majalisar Dokokin ta amince da buƙatar a yayin zamanta, wanda Kakainta, Abdul’aziz Garba-Gafasa ya jagoranta.
Wannan sahalewa ta zo ne kwana biyu kacal da Gwaman Ganduje ya aika da buƙatar.
A ranar Talata ne Kakakin Majalisar ya karanta wasiƙar da Gwamna Ganduje ya sanya wa hannu, wadda ta buƙaci a ba ƙananan hukumomi damar samun bashin, wanda za a karɓo daga GTBank.
‘Yan Majalisar sun amince da buƙatar ne bayan da Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye, Kabiru Hassan-Dashi, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar na Ƙananan Hukumomi ya gabatar da rahoton kwamitin.
Da yake bada dalilin da yasa suka amince da buƙatar, Shugaban Kwamitin ya ce: “Za a yi amfani da kuɗaɗen wajen gina ƙarin azuzuwa da yi wa wasu kwaskwarima don rage cunkoso”.
Mista Hassan-Dashi ya kuma ce bashin zai bada damar samar da sabbin kayan makaranta ga ɗalibai, da kuma tabbatar da ɗorewar shirin ciyarwa kyauta na gwamnati.
A wasiƙar da Gwamna Ganduje ya aika wa Majalisar Dokoki ranar Litinin, ya ce idan aka amince da ciyo bashin, kowace ƙaramar hukuma daga cikin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano za ta samu miliyan N340, da nufin tabbatar da ɗorewar shirin ilimi kyauta kuma wajibi a dukkan faɗin jihar.
Ya bayyana cewa za a biya bashin ne a cikin watanni 30, da kuɗin ruwa na kaso 15%.
A cewar wasiƙar, za a riƙe cire bashin ne daga kason kuɗi na wata-wata na ƙananan hukumomin da Gwamnatin Tarayya ke ba su.