Sarkin Ƙaraye Ya Ɗaga Darajar Mahaifin Kwankwaso Zuwa ‘Mai Naɗa Sarki’

171

Sarkin Ƙaraye, Ibrahim Abubakar II ya ɗaga darajar Musa Saleh-Kwankwaso, mahaifin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso zuwa muƙamin mai naɗa Sarki a sabuwar masarautar.

Majiyarmu ta bada rahoton cewa an ɗaga darajar dattijo Kwankwaso daga Majidaɗi zuwa Makaman Ƙaraye kuma Mai Naɗa Sarki.
Labarai24 ta bada rahoton cewa dama Mista Saleh-Kwankwaso shi ne Hakimin Madobi tun kafin a raba Masarautar Kano.

Wannan dai yana nufin a halin yanzu Hakimin Madobi yana ɗaya daga cikin mutane ƙalilan da za su iya zaɓar sarki a Masarautar Ƙaraye.

Masarautar Ƙaraye tana ɗaya daga cikin masarautu huɗu waɗanda ake ce-ce-ku-ce a kansu, waɗanda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ƙirƙira ranar 8 ga watan Mayu, 2019. Sairan su ne Bichi, Gaya da Rano.

Ana ganin ƙirƙirar sabbin masarautun dai a matsayin wani yinƙuri na rage tasirin Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, wanda suke da bambancin siyasa da Gwamna Ganduje.

A wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Masarautar, Haruna Gunduwawa ya aika wa jaridar Kano Focus, ya ce an ɗaga darajar Mista Kwankwaso ne sakamakon “gwaggwaɓar gudunmawa mara gajiyawa ga ci gaban masarautar mai ɗorewa” da yake bayarwa.

Yayinda yake taya Makaman Ƙarayen kuma Mai Naɗa Sarki, Sarki Abubakar II ya hore shi da ya ba maraɗa kunya.

A cewar sanarwar, kwanan ne za sa sanar da ranar da za a yi bikin naɗin Mista Kwankwaso.

Ɗan shekara 97, marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero ne ya naɗa Musa Saleh-Kwankwaso a matsayin Majidaɗin Kano kuma Hakimin Madobi a shekarar 2000.

Turawa Abokai

3 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan