Shugaba Buhari Ya Shiga Ganawar Sirri Da Goodluck Jonathan

301

Wasu rahotanni daga fadar shugaban ƙasa, sun bayyana cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dira fadar domin yin wata ganawar sirri da shugaba Muhammadu Buhari.

Mai magana da yawun shugaba Buhari, Femi Adesina, ya wallafa hotunan ganawar shugabannin biyu a shafinsa na Facebook.

Sai dai Femi Adesina bai yi bayani ba kan abin da shugabannin guda biyu suka tattauna a yayin ziyarar.

Wannan ne dai karo na biyu da tsohon shugaban ke ziyarta shugaba Buhari a baya-bayan nan.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan