Shugaban kungiyar alkalan kotunan shari’ar musulunci na jihar Kano, mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, ya bukaci gwamnati da ta biya bashin kudaden alawus din da suke bin gwamnati na kusan kimanin shekaru biyu.
Ibrahim Sarki Yola ya yi rokon ne, a yayin taron bita na kwanaki biyu da bangaren shari’ar musulincin karkashin jagorancin alkalin alkalai ya shirya musu a jihar Kano.
ya ce” Akwai bukatar gwamnati ta yi duk mai yuwa domin ganin ta biya mu bashin da muke bin ta, saboda da yawa daga cikin alkalan muna cikin wani hali na rashin babu”
Ya kuma ce ” Kuma ina jan hankalin alkalan shari’ar musulinci da su kasance masu tsantseni matuka, domin kaucewa fadawa cikin rashawa, kuma suma masu kawo shari’a kotunan da su kauracewa neman al’farma maimakon hakan su rinka tsayawa iya gaskiyar su kawai”. Inji Ibrahim Sarkin Yola.
Taron wanda ya gudana a ranakun Laraba da Alhamis din nan, ya samu halartar masu ruwa da tsaki a bangaren shari’ar musulinci da kuma alkalan bangare daban-daban manya da kanana.
Dala FM Kano

[…] Muƙalar Da Ta GabataAlƙalai A Jihar Kano Na Fama Da Matsalar Tattalin Arziƙi –Alƙali Sarki Yola […]